Jiya Alhamis, uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan ta halarci bikin hada hannun matasa da yaran Sin da Amurka na shekarar 2025 mai taken “Bond with Kuliang” a ofishin kungiyar sada zumunci da kasashen ketare ta kasar Sin, inda ta kuma gabatar da jawabi.
Mai tsara shirin “Abokantakar Kuliang” Elyn MacInnis da abokinsa Luca Berrone, sun yi bayani game da shirin Kuliang da labaransu game da sada zumunta da hadin gwiwa a tsakanin al’ummomin Sin da Amurka. Haka kuma, sun bayyana godiyarsu ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, ganin yadda yake kulawa da matasa da yaran kasar Sin da na kasar Amurka, sun kuma bayyana cewa, za su ci gaba da ba da gudummawarsu domin karfafa zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.
- Buhari 1942 – 2025: Rayuwarsa, Rasuwarsa, Jana’izarsa, Da Ci gaba Da Ta’aziyya
- Binciken Jin Ra’ayoyin Jama’a Na CGTN: Rahoton Matsayar Japan Kan Tsaro Na Takala Na Nuna Hatsari Mai Girma Game Da Tsaro
A yayin bikin, wakilai daga kasar Amurka sun bayyana farin cikin kawo ziyara kasar Sin, tare da fatan cewa, za su kasance jakadu masu ba da gudummawar zurfafa zumuncin Sin da Amurka, da yada kyakkyawar zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.
Cikin jawabinta, Peng Liyuan ta ce, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shirin “gayyatar matasa da yara dubu 50 daga kasar Amurka zuwa kasar Sin cikin shekaru 5 masu zuwa domin yin mu’amala da karawa juna sani”, kuma yanzu, bayan sama da shekara daya, matasa da yaran kasar Amurka da dama sun kawo ziyara kasar Sin, inda suka gane wa idanunsu harkokin kasar, tare da sada zumunci da takwarorinsu na kasar Sin. A nan gaba kuma, za su hada kai wajen bayyana kyawawan labaran zumuncin dake tskanin Sin da Amurka.
Ta kara da cewa, matasa da yara su ne manyan gobe, wadanda za su ba da gudummawar raya kasa da sada zumunci a tsakanin sassa daban daban. Inda ta ce suna fatan za su inganta zumuncin dake tsakanin Sin da Amurka, da kafa gadar zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, ta yadda za su kafa kyakyyawar makomar kasashen biyu. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp