Uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta halarci taron abokan zama na shugabannin kasashen G20 da uwargidan shugaban Indonesia, Iriana Joko Widodo ta shirya da safiyar yau a Bali.
Bisa rakiyar Iriana Joko Widodo, Peng Liyuan ta ziyarci wuraren nune-nunen kayayyakin waka da tufafi da sakar rattan da surfani da cimaka irin na gargajiya, inda ta ga wasu fasahohin hannu na gargajiya na kasar.
Peng ta yaba da yadda aka hada fasahohin hannu na gargajiya da aikin karfafa gwiwar mata da yaki da talauci da kare muhalli, tana mai cewa, kasashen biyu za su karfafa musaya da hadin gwiwa a bangarori masu ruwa da tsaki da bayar da gudunmuwa wajen yaki da talauci da kare muhalli a shiyyarsu. (Fa’iza Mustapha)