Yayin ziyararsa a kasar Indiya kwanan nan, shugaban kasar Philippines ya bayyana cewa, idan Sin da Amurka suka yi taho-mu-gama kan batun yankin Taiwan, Philippines ba za ta iya killace kanta daga ciki ba. Irin wannan furucin nasa yana da ban mamaki, wanda ya saba da alkawarin da Philippines ta yi na tsayawa ga manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kana, zai kara illata dangantakarta da kasar Sin, da zaman lafiya da tsaro a wannan shiyya.
Rura wutar rikici kan yankin Taiwan, yunkuri ne da Philippines ta yi na dogaro kan Amurka tare da ba ta hadin-kai, don hana ci gaban kasar Sin. Amma batun da ya shafi yankin Taiwan, batu ne na cikin gidan kasar Sin, kuma yadda za’a daidaita batun, harka ce ta al’ummar kasar zalla. Furucin shugaban Philippines ya saba da dokokin kasa da kasa da tsarin mulki na kungiyar ASEAN, tare da kawo babbar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin shiyyar gami da muradun jama’ar Philippines. Mai yiwuwa dogaro kan Amurka zai iya kwantar da hankalin gwamnatin Marcos ta Philippines, amma hakikanin gaskiya shi ne, za ta girbi abun da ta shuka. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp