Hukumar kididdiga ta kasar Sin da kungiyar masu jigila da sayayya ta kasar, sun fitar da bayanai a yau Laraba 1 ga wata, inda suka bayyana cewa, a watan Fabrairu, alkaluman sayayya na kasar Sin (PMI) sun karu zuwa kashi 52.6 cikin 100, a hannu guda kuma karuwar harkokin masana’antu ta ci gaba da fadada.
Zhao Qinghe, babban jami’in kididdiga na cibiyar binciken masana’antu ta hukumar kididdiga ta kasa, ya bayyana cewa, a watan Fabrairu, an kara ganin tasirin manufofi da matakan daidaita tattalin arziki, kuma tasirin annobar, da sauran abubuwan da ake zato duk sun ragu. Bugu da kari, an kara saurin dawo da harkokin samar da kayayyaki da kasuwanci na kamfanoni, kana makomar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ta ci gaba da karuwa.
Ana sa ran kasuwa za ta ci gaba da inganta. A watan Fabrairu da muke ciki, ana saran alkaluman ayyukan samar da kayayyaki da na gudanarwa su kai kashi 57.5 cikin 100, karuwar maki 1.9 sama da na watan da ya gabata, kuma ya tashi zuwa matsayi mafi girma a cikin kusan watanni 12. Imanin da ake da shi kan kasuwancin ya ci gaba da karuwa. (Mai fassara: Ibrahim Yaya)