Kamfanin jiragen sama na kasar Morocco ya karfafa tawagar ‘yan wasan kasarsa da karin jirage 30 na jigilar magoya bayan tawagar zuwa kasar Qatar a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya mai tarihi da za ta buga da kasar Faransa (France).
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, kamfanin ya ce, “Don ba da dama ga yawancin ‘yan Morocco da ke son tallafawa tawagar kasar a wasan daf da na karshe na gasar cin kofin duniya, Royal Air Maroc ya hada karfi da kasar Casablanca da Doha – Babban birnin Qatar.”
Ku tuna cewa Morocco ta doke takwararta ta Portugal – kasar Cristiano Ronaldo da ci 1-0 a ranar Asabar, inda ta zama tawaga ta farko a Afirka da ta samu tikitin shiga matakin kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya, wanda hakan yasanya farinciki a nahiyar Afirka baki daya.