Jimillar kudin tukuici da za a rabawa kasashen da suka halarci gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar sun kai dala miliyan $440.
Akwai kasashe 32 a gasar – kasashe 13 daga Turai, biyar daga Afirka, hudu daga kasashen Arewacin Amurka, hudu daga kasashen Kudancin Amurka sai kuma kasashe shida daga Asiya.
Kungiyoyin da suka fice daga gasar cin kofin a rukunin farko – Costa Rica, Serbia, Cameroon, Ghana, Uruguay, Denmark, Tunisia, Canada, Belgium, Jamus, Qatar, Ecuador, Wales, Iran, Mexico, da Saudi Arabia – kowannensu zai samu dala miliyan $9.
Kasashen da suka kai zagaye mai kasashe 16 – Spain, Japan, Switzerland, Koriya ta Kudu, Amurka, Senegal, Australia, da Poland – kowannensu zai samu dala miliyan $13.
Kasashen da suka fafata a zagaye na daf da na kusa da na karshe (Quarter final) – Brazil, Netherlands, Portugal, da Ingila – kowannensu zai samu dala miliyan $17.
Kasar Morocco wacce tazo ta hudu za ta samu dala miliyan $25
Wanda ya zo na biyu tsakanin Argentina da Faransa zai samu dala miliyan $30, yayin da wanda ya lashe kofin zai samu dala miliyan $42.