Tun bayan da Gwamnatin Tarayya ta ayyana cire tallafin man fetur, ranar 29 ga watan Mayun 2023, ake ta fuskantar cece-kucen yan Nijeriya dangane da tsadar rayuwar da matakin zai janyo sakamakon matakin, wanda suka hada da tashin farashin gwauron zabi da kayan abinci, kayan masarufi hadi da na sufuri da makamantan su, suka yi wadanda suka shafi rayuwar yau da kullum. Kana kuma da sabatta-juyen kwan-gaba kwan-baya da ke ci gaba da gudana tsakanin gwamnatin tarayya da yan kwadagon.
‘Yan Nijeriya sun nuna rashin gamsuwarsu da matakin cire tallafin man inda suka bayyana shi a matsayin wanda ba a yi dogon lissafi wajen aiwatar dashi ba a daidai irin wannan lokaci, wanda tsadar rayuwa ke neman zama tamkar auren-zobe a wuyan yan kasar, al’amarin da ya hadu da tasirin matsalolin tsaron da suka mamaye wasu sassan kasar, tare da mayar da hannun agogo baya a yanayin rayuwar al’ummar Nijeriya.
- Me Ya Sa Aka Kasa Shawo Kan Matsalar Hare-haren Bindiga A Kasar Amurka?
- Kwamishinan Benue Ya Kubuta Bayan Sace Shi Da Kwana 10
Daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa satin karshe na watan Satumban 2023, kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) tare da takwararta gamayyar kungiyoyin yan kasuwa (TUC) suka yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani, tun daga ranar 3 ga watan Oktoban wannan shekara, sannan duk da yake akwai tazarar watanni hudu tsakanin wannan lokacin, amma har yanzu ana yiwa juna kallon hadarin kaji; tsakanin Gwamnatin Tarayya, kungiyoyin kwadago da kuma yan Nijeriya a gefe guda.
A farkon watan Yuni, kungiyar NLC ta bayyana aniuarta wajen shiga yajin-aiki sakamakon karin farashin man fetur, biyo bayan cire tallafin man tare da barwa yan kasuwa wuka da nama a harkokin man fetur, wanda bisa ga alamu, yan Nijeriya sun fara tunanin samun fatan shawo kan wannan matsala, musamman lokacin da gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a shirye take wajen gudanar da tattaunawa da kungiyoyin kwadago domin gano bakin zare.
A ranar 5 ga watan Yuni ne tawagar gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Hon. Femi Gbajabiamila, yayin da kuma ya gana da kungiyar kwadago inda aka cimma matsayar amincewa da bullo da muhimman hanyoyin da zasu rage radadin da cire tallafin man fetur ya haifar ga yan kasa. Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya kungiyoyin kwadago (TUC da NLC) sun cimma matsayar kafa kwamitin hadin gwiwa da zai duba shawararin karin albashi ga ma’aikata tare da samar da ingantaccen shirin yadda za a aiwatar da al’amarin.
Bugu da kari kuma, ya kara da cewa, gwamnatin tarayya tare da kungiyoyin kwadago na TUC da NLC su sake duba tsarin bayar da kudaden tallafin bankin duniya tare da bayar da shawarar shigar da masu karamin karfi a cikin shirin, domin rage wahalhalun da janye tallafin zai jawo.
Wannan sabatta-juyen bata tsaya nan ba, wanda a wani taron da ya gudana tsakanin bangarorin, a tsakiyar watan Yuni, ya cimma matsayar yanke shawarar cewa ya kamata a dora wa Majalisar Harkokin Tattalin Arzikin Kasa (NEC) aikin tsara matakan da zasu saukaka wa yan Nijeriya radadin cire tallafin man. Wanda daga bisani aka zartas da cewa a danka wa gwamnatocin jihohi alhakin kula da matsalar jindadin al’ummar su, tare da amincewa cewa Gwamnatin Tarayya za ta bai wa kowace jiha Naira biliyan 5 a matsayin tallafin man fetur. Al’amarin da tun daga wannan lokacin jihohin suke yamadidin cewa suna raaba wa jama’a kayan abinci da makamantan su da sunan tallafin, wanda a nan ma tamkar an gudu ne amma ba a tsira ba.
Cire tallafin man fetur ba tare da kara wa ma’aikata albashi ba, kana ba tare da la’akari da halin da zai jefa talakan Nijeriya ba, ya samar da babban gibi da kara ya jawo mummunan hauhawan farashin kayan abinci da na masarufi, kana da man fetur din shi kansa wanda ya koma 630 maimakon 230 a baya, kuma sakamakon haka kudin sufuri suka ninka. Wanda yanzu haka talaka ko karamin ma’aikaci albashin sa ba zai wuce masa kwana 10 ba, ya kare, sai dai ya hada da bashi. Wannan shi ne lokaci mafi muhimmanci da ya dace kungiyoyin kwadago su matsa kaimi domin kwatowa ma’aikata tare da yan kasa yanci, sai dai kash, har yau bata canja zani ba.
Wani abin daure kai da mamaki shi ne, wadanne batutuwa ne ake tattaunawa tsakanin tawaar Gwamnatin Tarayya da shugabanin kungiyoyin kwadagon kan wannan batu a cikin watanni hudu da suka gabata, wanda har yanzu babu na kamawa a aikace? Sannan kuma shin wai me kungiyoyin kwadagon suke gayawa mambobinsu, wanda ya sha bamban da na shekaru takwas, na tsohowar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a lokacin Kwamared Ayuba Wabba ke shugabantar kungiyar NLC? A hannun guda kuma, masu iya magana sun ce: da na gaba ake gane zurfin ruwa.
A baya zamanin gwamnatin Mista Obasanjo, lokacin da Adams
Oshiomhole yake Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya (NLC), inda ya rinka wasan kura da tunanin yan Nijeriya wajen fitowa a kan titi yana kumfan bakin daukar matakan shiga yajin-aiki a wancan lokacin, inda ya gajiyar da gwiwoyin ma’aikatan da basu gano dawan garin ba, kafin shima daga bisani ya rikide zuwa babban jigo a harkokin siyasa- bayan da barazana mai cike da rudanin ya zamar masa tsani. Saboda ko shakka babu, biri ya yi kama da mutum, ganin cewa akwai alamar anya babu lauje cikin rawanin kungiyar kwadago, ko wani abu mai kama da hadin baki tsakanin su da gwamnati a kowane mataki, ko zama abokan tafiya tare da shirya wasan kwaikwayo a duk lokacin da suka jefa kasa cikin matsalolin tattalin arziki, inda cikin tasku a bar ma’aikata cikin hayaniya ita kuma gwamnati sai ta mayar dasu kamar karan kada miya.
Idan mutum ya tsaya tsam, abubuwan da zasu rika kai-komo a tunanin da shi ne, shin me yasa har yanzu kungiyar kwadago ta kasa takawa Gwamnatin Tarayya birki ga dukkan kudurorin ta; musamman abu mafi munin da zai jefa rayuwa cikin mawuyacin hali; cire tallafin man fetur, ace har yanzu babu abin kamawa. Al’amarin nan fa ya fara gundurar yan Nijeriya tare da jawo alamomin tambaya tsakanin Yan Kwadago da Gwamnatin Tarayya- anya ba Danjumma ne da Danjummai ba, musamman irin yadda cikin watanni hudu, kungiyar kwadago ta kasa samar da sauyin da sassaucin rayuwar da ya dace ma’aikata da sauran al’ummar Nijeriya su samu. Saboda hatta tallafin da mafi yawan gwamnatocin jihohi suka raba ba a bai wa ma’aikatan wani abin da zai taka kara ya karya bane.
A wani batu na daban kuma, ba a maganar rassan kungiyar kwadago na jihohi, su kam tun a tashin farko gwamnatocin Suka mayar dasu yan amshin Shata. Saboda hatta karin 25,000 ko 35000 da ake sa ran Gwamnatin Tarayya zata yi, bai shafi na jihohin ba- domin abu ne mai wahalar gaske kungiyar kwadago a matakin jihohi su ce uffan. Sannan kuma gwamnatocin jihohi zai yi wahala su saurari uwar kungiyar ta kasa, kaga kenan sai dai Allah ya jikan ma’aikatan jihohin.
A wata dabaran da Gwamnatin Tarayya ta yiwa kungiyar kwadago shi ne, ta bayyana cewa yajin aikin da kungiyar ta shirya yi ranar 3 ga watan Oktoba, bijirewa umarnin kotu ne, yayin da ita kuma gogar taka; kungiyar kwadagon ta bayyana cewa babu abin da zai taka mata birki a wannan karon, tare da yiwa gwamnati ba’a da cewa: bayan mari kuma harda tsinka jaka, ko kuma ya za a daki mutum kuma a hana shi kuka. Amma dai haka zancen ya wuce, sai dai kuma a jira wani jikon.
Tun da farko, shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) Mista Osita Chidoka, wanda tsohon ministan sufurin jiragen sama ne, ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara daukar matakai cire harajin bankuna da biyan tsuffin ma’aikata yan fansho.
Mista Osita ya bayyana hakan ne ranar Lahadin da ta gabata a wata hira da gidan Talabijin Channels, ya ce matakan da aka ambata za su taimaka wajen rage wahalhalun da yan Nijeriya ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur, biyo bayan cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar kwadago da Gwamnatin Tarayya a barazanar da suka yi ta bayan nan ta shiga yajin aiki.
A nashi bangaren, Babban Lauyan kare hakkin dan Adam, Mista Femi Falana, ya ce kungiyar kwadagon Nijeriya (NLC) tare da sauran kungiyoyin suna da damar tafiya yajin aikin da gudanar da zanga-zangar kamar yadda suka tsara, yana mai cewa hakan bai zama karan-tsaye ga umurnin kotu ba, sabanin abin da gwamnatin tarayya ta nuna.
Lauya Falana shi ne lauyan kungiyar kwadagon, ya bayar da hujjar cewa babu wata kotu a kasar wadda ta fitar da wata dokar da ta hana ma’aikatan Nijeriya shiga zanga-zangar lumana wadda kungiyar kwadago ke shirin gudanarwa.