Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya yi ta’aziyar rashin jami’an tsaron da suka rasa rayukansu a lokacin da suke fafatawa da ‘ yan bindiga a Æ™aramar hukumar Faskari.
Wannan lamari dai ya faru ne a daidai lokacin da jami’an tsaro suke bai wa manoma kariya domin girbe amfanin gonakinsu, sai ‘yan bindiga suka farmake su.
- Kasar Sin Na Kokarin Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaba A Duniya
- Zulum Ya Gabatar Da Ƙarin Kasafin Kuɗi Naira Biliyan 61 Ga Majalisar Borno
A cikin wata sanarwa da sakataren yaÉ—a labarai na gwamnatin, Ibrahim Kaula Muhammad, ya fitar, ya ce jami’an tsaron sun rasa rayukansu ne a lokacin wani É—auki ba daÉ—i da ‘yan ta’adda.
A cewarsa, dakarun tsaron C-Watch gudu hudu sun mutu a yayin da ‘yan banga guda biyu suka kwanta dama.
“Hakika akwai takaici na rasa waÉ—annan jarumai, sai dai ina yabawa kokarin jami’an tsaron da suka dauki matakin dakile wannan farmaki wanda hakan ya tseratar da rayuka da dama.”
Sanarwar ta Æ™ara da cewa Æ™oÆ™arin da jami’an tsaro suka nuna musamman ‘yansanda da sojoji ya Æ™ara taimakawa wajen ceton al’ummar daga ‘yan bindigar da suka yi wa yankin Æ™awanya a wannan lokaci.
Gwamnan ya ƙara bayar da tabbacin kokarin gwamnatinsa ke yi na samar da tsaro a wannan yanki.
Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa waÉ—anda suka rasa ransu za a daÉ—e ba a manta da su ba, musamman ganin yadda suka sadaukar da ransu wajen kare al’umma da duniyoyin su
Gwamnan ya nanata kudirin gwamantinsa, na samar da jin dadi da walwalar al’ummar Jihar Katsina.
Sannan ya yi kira ga sauran al’umma da suka kasance cikin shiri da lura akan duk wani abu da masu amince da shi ba, sannan su cigaba da baiwa hukumomin tsaro goyan baya domin a samu nasarar da ake buÆ™ata.