Wasu gidajen mai da ‘yan kasuwa masu sayar da kayan mai hadi da masu hulda da matatar man Dangote suna ta kulle gidajen mansu na wucin-gadi na tsawon kwanaki sama da biyar biyo bayan rage farashin litar mai da matatar man mai fitar da gangan 650,000 a kowace rana ta yi.
Rahotonni sun bayyana cewar gidajen man MRS da ke Abuja a kan babban hanyar Kubwa, da wasu gidajen mai ba su sayar da mai tun lokacin da matatar Dangote ta sanar da rage farashin litar mai zuwa naira 835 a ranar Talata 16 ga watan Afrilu.
- Uwargidan Shugaban Kasar Sin Ta Tattauna Da Takwararta Ta Kasar Kenya
- Idan Kana Son Barin PDP, Yanzu Ne Lokacin – Bukola Saraki
Wani ma’aikacin MRS wanda ya nemi a sakaye sunansa saboda ba shi ne aka amince yake maganar da yawun gidan Man MRS ba, ya shaida wa majiyarmu cewa gidan man na fuskantar asara muddin ya sayar da mansa a sabon farashin Dangote.
“Saboda ragin farashin litar man fetur da Dangote ya yi ne. Gidan man yana da tsohon mai da ya saya a farashin da ya fi wannan, kuma ba zai sayar da shi a asara ba.
“Wannan dalilin ne ya sanya muka rufe gidajen man tun ranar Talata. Da yiwuwar mu bude nan gaba.”
Kazalika, wani ma’aikacin gidan man, ya tabbatar da cewa suna ‘yan wasu gyare-gyare ne amma za su sake budewa. Ya kuma ce, gidan man zai fara sayar da man fetur ga jama’a a ranar Talata kan kudi naira 910 a kowace lita.
Rahotonni sun tabbatar da cewa sauran abokan huldar matatar man Dangote, kamar su AP, Ardoba, da Optima, sun yi ta sayar wa jama’a da fitar kan kudi tsakanin naira 910 zuwa 920 kan lita guda a wasu sassan Abuja zuwa ranar Litinin da ta gabata.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan lamarin, shugaban kungiyar Dillalan Mai a Nijeriya, Billy Gillis-Harry, ya ce, saukan farashin man fetur ya shafi karfin sayen mai na dillalai da ‘yan kasuwa.
A cewarsa, yawan sauka da tashin farashin mai ba abu ne mai dadi ga sashin mai da kuma tattalin arzikin Nijeriya ba, “Ba abu ne mai kyau ga kasuwanci da tattalin arziki da ma ‘yan Nijeriya ba.”
A baya dai Gillis-Harry ya taba yin kiran da a shafe sama da watanni shida a kan farashin fetur ba tare da canji ba domin kyautata harkokin kasuwancinsa.
Shi kuma mai magana da yawun kungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya ce masu gidajen mai suna da fetur da suka sayo a tsohon farashi ne, kuma matakin matatar Dangote na rage farashin zai sanya su tafka asarar biliyoyin naira.
A baya-bayan nan ne Kamfanin Man Fetur na Nijeriya ya rage farashin ga dillalansa zuwa naira 935 ga kwastomomi a Abuja a matsayin martani ga sabon rage farashin matatar man Dangote.
Hakan na nufin a halin yanzu ‘yan Nijeriya na sayen man fetur a tsakanin naira 890 zuwa naira 950 kan kowace lita.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp