Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata mai wakiltar Yabe ta Arewa, Dr. Ahmad Lawan, ya tallafa wa al’ummar mazabarsa da kayan abinci kimanin buhuna 9000 na hatsi da shinkafa don rage radadin tsadar rayuwa a yankin.
Wannan matakin tallafin na Sanata Lawan, dadi ne a kan makamancinsa wanda Gwamnatin Tarayya da ta jihar Yobe ke yi wajen ragewa al’umma wahalhalun da suke fuskanta, sakamakon cire tallafin man fetur.
- Yanzu-yanzu: Sanata Ahmed Lawan Ya Lashe Mazabarsa A Yobe Ta Arewa
- Dalilinmu Na Karbar Sunan Ahmed Lawan Maimakon Na Machina – INEC
Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya kaddamar da tallafin kayan abincin, wanda Gidauniyar ‘SAIL’ ta dauki nauyin aiwatar da shi a cikin gundumomi 60 da ke Yobe ta Arewa.
Taron rabon kayan tallafin abincin ya gudana ne ranar Asabar, a Filin Kwallon Kafa da ke unguwar Katuzu a garin Gashuwa ta karamar hukumar Bade a jihar Yobe; wanda ya kunshi buhunan shinkafa 6000 da na gero 3000.
An raba tallafin ga kungiyoyin addinin musulunci, na Kirista, nakasassu da masu karamin karfi daga kananan hukumomi shida na Yobe ta Arewa. Bade, Nguru, Jakusko, Karasuwa, Yusufari da Machina.