Sana’ar watsa labarai ta kasar Sin ta shiga wani zamani na zurfafa cudanyar fasahohin zamani da basira, a cewar rahoton sana’ar da aka fitar a yau Talata.
Kungiyar ’yan jarida ta kasar Sin ce ta hada rahoton mai taken “Ci gaban kafofin watsa labaru na kasar Sin (2024)”.
Rahoton ya ce kirkirarriyar basira ta generative AI ta haifar da sauyi wajen tattara labarai da samar da su, da habaka salon gudanar da ayyukan jarida da sadarwa. (Mohammed Yahaya)