Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce rahoton da gwamnatin Amurka ta fitar game da aiki da matakan shawo kan yaduwar makamai, tamkar ba’a Amurkan ta yiwa kanta.
Jami’in wanda ya bayyana hakan, yayin taron manema labarai na yau da kullum da aka saba gabatarwa, a yau Jumma’a ya ce wancan rahoto na shekarar nan ta 2025 da ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ta fitar, dangane da shawo kan makamai, da hana yaduwarsu, da kwance damararsu ya saba wa gaskiya, kasancewar a zahiri Amurka ce kasa mafi yin watsi da tsarin da ake bi na shawo kan samarwa, da hana bazuwar makamai.
Guo Jiakun, ya kara da cewa cikin shekaru masu yawa gwamnatin Amurka ta ci gaba da kawar da kai daga gaskiya, tana tsara wannan rahoto maras tushe. A maimakon ta yi duba kan munanan ayyukan da take gudanarwa a fannin samarwa, da kwance damara, da hana yaduwar makamai, gwamnatin Amurka ta sauya gaskiya, tare da zargin wasu kasashe ba tare da wata hujja ba, wanda hakan dabara ce ta babakere da yin fuska biyu.
Bugu da kari, game da amincewar da gwamnatin shugaba Trump ta yi da aikin hako ma’adinan karkashin teku, Guo Jiakun ya ce ba wata kasa dake da ikon karya dokokin kasa da kasa a wannan fanni, ta yadda za ta iya keta dokokin bincike, da bunkasa ayyukan hako ma’adinan karkashin teku ba bisa ka’ida ba, domin kuwa hakan zai haifar da illa ga moriyar daukacin al’ummun kasa da kasa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp