Gwamnatin Jihar Jigawa a ranar Juma’a ta ce, za ta ciyar da mutane 171,900 a kullum a cikin watan Ramadan.
Gwamna Umar Namadi, wanda ya bayyana haka a wajen bikin raba kayan abinci a birnin Dutse ta jihar Jigawa, ya ce jihar na da burin ciyar da mutane miliyan 5,157,000 a tsawon watan Ramadan.
- Gwamnatin Jigawa Za Ta Raba Kayan Abinci Don Rage Raɗaɗin Tsadar Kaya Da Azumi
- Tsadar Rayuwa: Yadda Aka Kama Manyan Motoci 4 Na Kayan Abinci A Jigawa
Ya ce, jihar ta samar da cibiyoyi guda biyu a kowace mazabar zabe domin gudanar da shirin, inda ya kara da cewa kowace cibiya ana sa ran za ta ciyar da mutane akalla 300 a kullum, wanda ya kai 171,900 a kowace rana a cibiyoyi 573.
Namadi ya ce, an fara shirin ciyar da mabukata a lokacin azumi.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin saukaka wani tsarin tallafin da shugaban kasa, Bola Tinibu, ya yi wa al’ummar Jigawa.
Don haka, ya tabbatar wa ‘yan jihar cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen ciyar da su, musamman a halin da ake ciki na matsin rayuwa a kasar nan.
Tun da farko, kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Auwalu Sankara, ya ce za a raba jimillar buhunan shinkafa 25,000 da buhu 150,000 na masara 25kg da kuma katon na taliya 100,000 ga magidanta 150,000.
Sankara ya ce, gwamnatin jihar ta yi tanadi ga mutane 700,000 da za su ci gajiyar tallafin a fadin kananan hukumomin jihar 27.