A kokarin ganin al’ummar musulmin jihar Sokoto sun fara azumin watan Ramadan na bana cikin nutsuwa da walwala, Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da biyan kyautar rabin albashi ga daukacin ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a jihar.
Wannan gagarumin karamcin, a cewar wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ya rabawa manema labarai a daren Lahadi, ta ce, biyan rabin albashin ga ma’aikatan jihar, an yi ne domin saukakawa ma’aikatan wajen gudanar da azumin watan Ramadan na bana cikin sauki.
Don haka, Gwamna Aliyu ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da watan Ramadan mai alfarma wajen addu’ar Allah ya kawo mana tallafi kan dimbin kalubalen da suka addabi Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp