Sanata Abdulaziz Yari, mai wakiltar Jhar Zamfara ta yamma, na shirin raba tirela 358 na kayan abinci iri-iri daban-daban.
Kayayyakin da za a raba sun hada da; shinkafa da gero da suga da masara.
- Abdulaziz Yari Ya Bada Tallafin Tirela 240 Na Abincin Azimi A Zamfara
- Yari Ya Lashe kujerar Sanatan Zamfara Ta Yamma
Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Kungiyar Siyasa ta A Yari, Ibrahim Muhammed, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Gusau a ranar Lahadi.
Ya ce za a raba kayan abincin da aka ne don taimakawa mutane wajen gudanar da azumin watan Ramadana ga kowa da kowa ba tare da la’akari da bambancin ra’ayin siyasa ba.
A cewarsa, an shirya tsarin rabon a karkashin kungiyar siyasa ta A Yari bisa jagorancin Lawal Limana wanda ake sa ran magidanta 17,500 za su ci gajiyar rabon.
Muhammad ya bayar da tabbacin cewa kananan hukumomi 13 cikin 14 na jihar za su ci gajiyar shirin.
Ya bayyana cewa sama da kashi 98 cikin 100 na kayayyakin tuni an yi nasarar jigilarsu zuwa kananan hukumomi daban-daban na jihar, wanda hakan ya sa wadanda za su ci gajiyar tallafin za su samu nasu kason kan lokaci.
Shugaban kwamitin yada labaran ya bayyana wadanda za su ci gajiyar tallafin, wadanda suka hada da; mabukata da marayu da zawarawa da sauransu.
Muhammad ya tabbatar da cewa za a fara rabon kayan abincin kafin watan Ramadan, ya kuma bukaci jama’a da su yi wa tsohon gwamnan da jihar da kuma kasa baki daya addu’a.