Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero ya yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi da su rage tsadar kayan abinci da sauran kayayyaki domin bai wa talakawa damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Zariya a lokacin bikin kaddamar da wani littafi mai suna: “Dauloli a Kasar Hausa” ma’ana ‘Masarautu a kasar Hausa’ na Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau.
Ado-Bayero ya kuma shawarci ’yan Nijeriya masu hannu da shuni da su rika taimakawa marasa galihu a lokacin azumin Ramadana.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya kare rayukan al’umma su shaida wannan wata mai alfarma cikin koshin lafiya tare da yin addu’o’i a watan.
Sarkin ya yabawa mawallafin littafin, da ya yi bayani dalla-dalla kan masarautun Hausa a Kano da Katsina,l da Zamfara da Kebbi da Zazzau da dai sauransu.
“Bayanan da aka ba da cikakken bayani kan tsarin gudanar da mulki da kowace masarauta da sana’o’insu da ka’idoji da dabi’unsu,” inji shi.
Mai nazarin littafin, Farfesa Ahmed Zaria na Jami’ar Jihar Kaduna ya ce littafin mai shafi 356 yana da babi bakwai.
Ahmed Zaria ya ce littafin ya ba da cikakken labari da tarihin masarautun Hausa da siyasarsu da tsarin mulki da ka’idoji da dabi’u tun daga kafuwarsa zuwa yau.
Ya kara da cewa littafin ya zama dole kan dalibai ya kasance suna da kwafinsa da masu bincike a fannin ilimin harshe da tarihi.
Mawallafin littafin, Farfesa Gusau ya ce, littafin wani ƙoƙari ne na daidaita rubutaccen tarihin Masarautun Hausa inda ya ce galibin binciken da ake yi a jami’o’in kan masarautu kaɗan ne ba duka ba.
Gusau ya kara da cewa littafin kuma wani yunkuri ne na tallafawa juna da karfafa hadin kai a tsakanin masarautun Hausa da sauran ‘yan Nijeriya.