A yau ne ɗaya daga cikin Malaman Musulunci da ke garin Kaduna, Shehu Isma’ila Umar Almaddah (Mai Diwani) ya buɗe Tafsirin Alƙur’ani Mai Girma na Azumin Ramadan na bana.
Shehu Isma’ila ya buɗe Tafsirin ne bayan gabatar da Sallar Azuhur a Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group da ke Layin Matazu kusa da Titin Kagoro da ke Sabon Garin Tudun Wada Kaduna.
Da yake gabatar da jawabi kafin shiga karatu, Shehu Isma’ila Umar Almddah ya yi godiya ga Allah da ya sa aka kammala zabukan Nijeriya lafiya tare da yin kira ga wadanda suka samu nasara su rungumi wadanda suka sha kaye domin ciyar da ƙasa gaba.
Sannan kuma, ya yi kira ga takwarorinsa Malamai da suji tsoron Allah, sun fahimci cewa, suna zaune ne akan kujerar Alqur’ani, don haka su sanar da al’ummar Annabi Muhammad SAW sakon da ke cikin Alkur’ani da sunnar Annabi SAW.
Bugu da kari, Malamin ya bayyana cewa, Alkur’ani yana magana da ilimin da yake a fili (zahiri) da wanda sai mai babban hankali (badini), wanda ya fahimci hakan zai kai Al’ummar Annabi SAW tudun mun tsira ba zai kaisu ga hallaka ba.
Kowane Malami ya dace ya yi adalci ya tsaya dai-dai iliminsa.
“Muna godiya ga Allah, shugabannin da aka zaba Allah ya yi musu jagoranci, su kuma wadanda ba su samu ba su yi haƙuri a tari gaba. Waɗanda suka samu nasara su nemi hadin kan wadanda ba su samu ba domin a haɗa karfi wuri guda wajen kawo ci gaban ƙasa.
“Kar waɗanda suka yi nasara su ɗauki abin da gayya, su riƙa yi wa wadanda ba su samu ba dariya. Su ja su a jiki domin a taru a yi wa ƙasa aiki. Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya, Allah ya kawo mana ci gaban ƙasa amin.” Ya bayyana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp