• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rana Ba Ta Karya: Habakar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Ba Mahassada Kunya

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

Idan muka kalli halin da duniya ke ciki a natse, za mu ga cewa, illolin da ke tattare da tsauraran manufofin kudi na manyan tattalin arziki sun yi fice. Hadarin dake tattare da rashin hadin kai, babakare, rikice-rikice na yanki da siyasar kasa da kasa suna karuwa, kuma tattalin arzikin duniya yana kara tabarbarewa. Amma duk da wannan barazanar, tattalin arzikin Sin na nan da karfinsa daram. 

Kar a yaudare ku da labarun karya, Jimillar GDP na kasar Sin ya karu da kashi 5.2 cikin dari a shekara zuwa yuan tiriliyan 126.06 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 17.71 a shekarar 2023, bisa ga bayanan da hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar. Sin ta ba da gudummawar sama da kashi 30 cikin 100 ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya tsawon shekaru a jere, tana matsayin gaba a cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya kuma a matsayin babbar injin ci gaban tattalin arzikin duniya.

  • Amurka Ta Zama Babban Cikas Ga Dakile Yakin Gaza Bayan Da Ta Hau Kujerar Na Ki
  • Aleksandar Vučić: Yarjejeniyar Ciniki Cikin ‘Yanci A Tsakanin Sin Da Serbia Ta Bude Sabuwar Kofa Ga Bunkasuwar Serbia

Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ya samo asali ne sakamakon matakan da kasar ta dauka na daidaita fannonin tattalin arzikinta. A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta aiwatar da matakan bude kofa ga waje da dama, da rage tsauraran matakan shigowa cikin kasar, da inganta yanayin da ya dace ga kamfanonin waje don zuba jari a kasar. Yadda kasar Sin ke kara ci gaba, haka take kara bude kofarta, ta kasance abin dogaro ga masu zuba jari a duniya. Aiwatar da dokar zuba jari ga kasashen ketare da daidaita ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa sun kara inganta tsarin zuba jarin waje.

Fiye da kashi 80 cikin 100 na kamfanonin ketare sun gamsu da yanayin kasuwancin kasar Sin a bara, yayin da sama da kashi 90 cikin 100 suka yi imanin cewa, kasuwar kasar Sin na da armashi, a cewar wani rahoto kan sakamakon binciken da majalisar bunkasa harkokin cinikayya ta kasa da kasa ta kasar Sin ta wallafa.

Idan aka yi la’akari da tarihi, bunkasuwar kasar Sin wani babban dalili ne na ci gaban dukkan bil’adama. Kasar Sin ta yau ba ta Sinawa kadai ba ce, ta zama kasar Sin ta duniya baki daya. Yayin da adadin ci gaban kasar Sin ya karu da kashi daya cikin dari, ci gaban sauran kasashe ya karu da kashi 0.3 cikin dari, bisa ga binciken IMF. Kasar Sin na ci gaba da himmatuwa wajen inganta yanayin kasuwanci ga masu zuba jari, tana kara kaimi ga farfadowar tattalin arzikin duniya, yayin da mahassada ke jiran labarin rugujewar tattalin arzikinta. (Muhammed Yahaya)

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

October 25, 2025
Next Post
BUK

Dalibai 180 Sun Kammala Digiri Da Daraja Ta Daya A Jami’ar Bayero, Kano

LABARAI MASU NASABA

Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

October 25, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

October 25, 2025
Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.