Yau ranar Afirka ce ta 60, wadda ta tunatar da mutanen duniya nasarar da jama’ar kasashen Afirka suka samu, a kokarin kawar da kangin mulkin mallaka, da neman ‘yancin al’umma a tarihi.
Ba za mu taba mantawa ba, nahiyar Afirka ta taba juriyar wahalhalu na mulkin mallaka, da bautarwa, gami da danniya, da kasashen yamma suka yi mata, cikin shekaru fiye da 100.
Zuwa farkon karni na 20, kasashe masu karfi dake yammacin duniya sun riga sun raba kashi 95% na yankunan Afirka. Sa’an nan, bayan da aka kawo karshen yakin duniya na 2, sannu a hankali kasashen Afirka sun fara fid da kansu daga mulkin mallaka. Zuwa shekarar 1963, an kafa kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta OAU (wadda ta zama kungiyar tarayyar Afirka ta AU daga bisani), an kuma kebe ranar “‘yantar da Afirka” (wadda ta zamanto “ranar Afirka” yanzu). Daga baya kasashen Afirka sun yi ta kokarin hadin kai da juna, inda suke taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasa na duniya. Zuwa yanzu, ranar Afirka ita ma tana alamanta kokarin al’ummun kasashen Afirka na hadin gwiwa, da neman samun zaman lafiya da ci gaban kasashen nahiyar.
Wang Yi, shi ne babban jami’in kasar Sin mai kula da harkokin hulda da kasashen waje. Ya taba bayyana cewa, ranar Afirka tamkar ranar kasar Sin ce, wadda ta kasance biki na bai daya ga dukkan bangarorin Afirka da Sin.
Shin ko mene ne ya sa ya fadi haka? Dalili a nan shi ne tun daga shekarun 1950, jamhuriyar jama’ar Sin wadda ba ta jima da kafuwa ba a lokacin, ta riga ta fara mai da hankali kan kokarin al’ummun nahiyar Afirka na ‘yantar da kai, gami da ba su goyon baya a kai a kai. Inda kasar ta Sin ta sanar da ka’idoji biyar na zama tare cikin lumana, da ba da tallafin layin dogon da ya hada kasashen Tanzania da Zambia, da taimakawa kasashen Afirka wajen yakar mulkin mallaka da na danniya, gami da ba da taimako ga yunkurin kasashen Afirka na ‘yantar da kai, da daukaka matsayinsu a idanun al’ummun duniya.
Bayan haka kuma, kasar Sin ba ta taba ja da baya, a kokarin taimakawa kasashen Afirka wajen samun ci gaba ba. Gyare-gyare da bude kofa da kasar ta yi, da yadda ta yi kokarin raya masana’antu, sun sa tattalin arzikin Sin samun ci gaba cikin matukar sauri, gami da samar wa nahiyar Afirka da kayayyaki masu inganci da saukin farashi, ta yadda aka samu damar kyautata zaman rayuwar jama’ar kasashen Afirka.
Zuwa shekarar 2000, an kafa dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, wanda ya nuna cewa, hadin gwiwar Afirka da Sin mai amfanar junansu ya shiga wani sabon babi. Daga shekarar 2000 zuwa yanzu, a fannin gina kayayyakin more rayuwa kadai, kamfanonin kasar Sin sun gina, da sabunta layin dogo mai tsayin fiye da kilomita dubu 10, da hanyoyin mota na kimanin kilomita dubu 100, da gadoji kusan dubu 1, da tashohin jiragen ruwa kusan 100, da dimbin asibitoci da makarantu a kasashen Afirka, tare da samar da guraben aikin yi fiye da miliyan 4.5. Duk wadannan nasarori ne da suka samu yabo daga jama’ar kasashen Afirka.
Yanzu haka a nahiyar Afirka, wasu kasashe 27 sun riga sun shiga jerin kasashen da jama’arsu ke samun matsakaicin kudin shiga, bisa kididdigar da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fitar. Kana yankin ciniki mai ‘yanci mafi girma a duniya da aka kafa a shekarar 2018, wato yankin ciniki mai ‘yanci na Afirka ko (AfCFTA), yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da wata hadaddiyar babbar kasuwa a nahiyar Afirka, wadda ta shafi mutane kusan biliyan 1.3, da yawan jimillar GDP da ta kai dalar Amurka triliyan 2.5. Duk wadannan abubuwa sun zama tushe mai kyau ga yunkurin Afirka da Sin, na ci gaba da yin hadin gwiwa a wani mataki mai inganci.
A kwanan baya, babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya ce AfCFTA zai iya haifar wa kasashen Afirka da karuwar kudin shiga ta kashi 9%, zuwa shekarar 2035, wadda za ta fid da mutane kimanin miliyan 50 daga kangin talauci. Sai dai a cewarsa, don cimma wannan buri, ya kamata kasashen Afirka su samu karin rance, da jarin da ake zuba musu, da raya bangaren masana’antu, da karfafa ciniki a tsakanin kasashen Afirka, da kyautata kayayyakin more rayuwa a bangarorin makamashi mai tsabta, da fasahohi na zamani, da baiwa matasa da mata damar karatu, da samun gurbin aikin yi.
Bayan da na karanta maganar Guterres, nan take na fahimci cewa, kasar Sin za ta iya ba da taimako ga kasashen Afirka, kan dukkan bangarorin da aka ambata. Kana a lokacin da kasar Sin ke kokarin samar da taimako, kamfanoni da sauran hukumomin ta, su ma za su cimma burinsu na neman ci gaba. Ta haka za mu iya ganin yadda tsare-tsaren tattalin arziki na kasashen Afirka da kasar Sin, suke zama masu dacewa da juna, inda suke samun dimbin moriya ta bai daya a kokarinsu na raya kai.
A lokacin baya, kasashen Afirka da kasar Sin, sun yi kokarin neman ‘yancin kai, da kare mutuncin al’umma kafada da kafada. Sa’an nan a yanzu suna hadin gwiwa da juna a kokarin raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’a. Har kullum suna rufawa juna baya da sahihanci.
Duk wani ci gaban da nahiyar Afirka za ta samu, zai sa kasar Sin alfahari. Wannan shi ne dalilin da ya sa ake cewa “ranar Afirka tamkar ranar kasar Sin ce”. (Bello Wang)