Uwargidan Gwamnan jihar Katsina Hajiya Zulaihat Dikko Umar Radda ya jagorancin taron ranar ‘Polio’ ta duniya tare da sauran kungiyoyi a jihar Katsina
Da take magana a wajen taron wanda aka gayyaci wadanda suka kubuta daga wannan lalura ta shan Inna da sauran cututtuka ‘Polio Surbibers’
Hajiya Zulaihat Dikko Radda ta bayyana cewa kokarin da suke yi na ganin karshen cututtuka masu nakasa al’umma yana tafiya akan tsari a Nijeriya musamman jihar Katsina
Saboda haka ta yi kira ga iyaye su tabbatar da cewa yaran su sun karbi Allurar riga-kafin inda ta yi roko ga shugabanni gargajiya da su taimaka wajen ganin an cigaba da fadakar da al’umma akan wannan cututtuka.
Hajiya Zulaihat Dikko Radda ya bayyana cewa Nijeriya ta samu wadanda suka kamo da cutar shan Inna 70 a jihohi 14 da kananan hukumomi 46 shekarar 2024.
A cewar ta a cikin shekarar 2024 jihar Katsina kawai ta samu masu wannan cuta mutum 17 tare da guda biyu a karamar hukumar Danmusa a cikin wannan shekara
Haka kuma Hajiya Zulaihat Radda ya bada tabbacin cewa kowane yaro an tabbatar da ya amshi allurar Riga-kafin shan Inna
Ana jawabin wakilin asusun tallafawa yara na UNICEF na ofishin Kano, Rahama Mohammed Farah ta yabawa kokarin jihar Katsina na dawo da sabon yunkurin kawar cutar shan Inna a Nijeriya baki daya
Ya kuma bayyana cewa asusun kula da kananan yara na UNICEF Yana hadin gwiwa da gwamnatoci da hukumomi da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi domin ganin wajen fadakar da al’umma akan allurar Riga-kafin shan Inna a jihar Katsina.
Shima da yake jawabi shugaban hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina Dakta Shansudeen Yahaya ya yi alkawarin cigaba da wayar da kan al’umma akan wannan cuta ta shan Inna da sauran cututtuka masu kashe yara a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina
Wadanda suka shaida wannan bikin ranar ‘Polio’ ta duniya sun hada da hukumar lafiya ta WHO da kuma masu lalurar cutar shan Inna da wakilan asusun UNICEF da matan shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina
 
			



 
							








