Yau ce “Ranar Muhalli” ta farko ta kasar Sin. A cikin shekaru 18 da suka wuce, manufar “tsaunuka biyu” ba wai kawai ta yi babban tasiri kan gina wayewar kan muhalli na kasar Sin ba, har ma ta ba da gudummawar hikimar kasar Sin, da samar da mafitar kasar Sin, da nuna nauyin dake kan babbar kasa wajen tafiyar da harkokin muhallin duniya.
A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta kasance a kan gaba a duniya baki daya, wajen samar da makamashin da ake iya sabuntawa, wanda ke wakiltar hanyar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa da iska, da hasken rawa. Bugu da kari, wannan fanni ya zama wata alkibla mai muhimmancin gaske a aikace, tsakanin Sin da abokan huldar kasa da kasa, musamman kasashe masu tasowa.
Kasar Sin ta samu gagarumin sauyi, daga matsayin mai shiga a dama da ita a harkokin kula da muhalli na duniya, zuwa jagora ta hanyar daukar nauyin babbar kasa, da nuna nauyin dake bisa wuyanta a matsayinta na babbar kasa.
Game da “Ranar Muhalli”, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Talata 15 ga wata cewa, yau ta kasance ranar muhallin halittu ta farko ta kasar, wadda ta shaida muhimmancin kiyaye muhallin halittu a sabon zamanin da muke ciki, gami da babbar aniyar kasar, a fannin raya kasa mai kyan muhalli, da shaida babban matsayin kasar ta Sin, na halartar ayyukan kiyaye muhalli, da daidaita yanayi a duk fadin duniya, tare kuma da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Masu Fassarawa: Ibrahim Yaya, Murtala Zhang)