A game da yadda wasu kafofin watsa labaru na yammacin duniya suka yi ta yin katsalandan a kan gyare-gyaren matakan yaki da annobar cutar COVID-19 da kasar Sin ta yi, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Larabar nan cewa, kalaman da abin ya shafa sun nuna son zuciya ne da neman bata sunan kasar Sin da kuma yin magudin siyasa bisa wasu dalilai na daban, wadanda suka saba gaskiya.
Wang Wenbin ya ce, tun bayan bullar cutar a cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta kan mayar da tsaron jama’a da rayukansu a gaban komai, tare da tattara dukkan albarkatu, da yin iyakacin kokari wajen kare rayuka da lafiyar dukkan Sinawa, da jure tasirin da annobar ta haifar daya bayan daya, kuma ya dace da yanayi mafi wahala lokacin da kwayar cutar ta yadu. A duniya baki daya, kasar Sin ce ta fi kowacce kasa karancin wadanda cutar ta yiwa illa da ma mace-mace.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, yadda ake kamuwa da cutar nau’in Ormicrone ya yi kasa sosai, yayin da karfin da kasar Sin ke da shi wajen yin magani, gano kwayoyin cutar da kuma rigakafi na ci gaba da inganta .
A game da wannan batu, kasar Sin ta dauki matakin inganta yaki da annobar bisa lokaci da yanayi, kuma sannu a hankali ta karkata akalarta daga rigakafin kamuwa da cutar zuwa ga kare mutane kamuwa da munanan cututtuka da kare lafiya. Wannan mataki ne na kimiyya da ya dace, akan lokaci kuma ya zama tilas. Manufar ita ce inganta tsaro da lafiyar jama’a da rage tasirin annobar kan ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.(Ibrahim)