Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi Allah-wadai da ci gaba da mace-macen yara kanana daga cututtukan da za a iya magance su kamar zazzabin cizon sauro, yana mai bayyana hakan a matsayin babbar gazawar shugabanci nagari.
Obasanjo wanda ya bayyana hakan a ranar Talata a wajen kaddamar da cibiyar kiwon lafiya ta CARE 365 a Abuja, ya ci gaba da cewa, ba za a amince da cewa, har yanzu miliyoyin ‘yan Nijeriya na tafiya mai nisa don samun kiwon lafiya, duk da ‘yancin kai da aka samu shekaru da dama.
Tsohon shugaban, wanda ya jagoranci kaddamar da cibiyar, ya ce, bayar da kiwon lafiya ba gata ga masu hannu da shuni ko mazauna birni ba ce kawai, hakki ne ga kowane dan Nijeriya.
Ya yaba da Cibiyar Kiwon Lafiya ta CARE 365 a matsayin “mai canza tsari” wanda za ta iya bayar da damar samun ingantacciyar lafiya kuma mai araha.