Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kira wani babban taron tsaro a yau Talata tare da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Nuhu Ribadu da babban hafsan tsaron kasa (CDS) Janar Christopher Musa, a fadar gidan Gwamnati da ke Abuja.
Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotonnin kashe-kashe da barnata dukiyoyi a sassan kasar nan, musamman a jihohin Filato da Benuwai.
- Yanzu-yanzu: Gwamnan Delta Oborevwori Ya Fice Daga PDP Zuwa APC
- Sabbin Haraji: Yadda ‘Yan Bindiga Ke Tilasta Wa Jama’a Biyan Miliyoyin Kuɗi A Zamfara
Shugaba Tinubu, wanda ya dawo daga ziyarar aiki ta kwanaki 19 a Turai a yammacin ranar Litinin, ana sa ran zai samu bayanai daga manyan jami’an tsaro da na leken asiri kan halin da ake ciki a yankunan da suka fuskanci tashe-tashen hankula da zubar da jini a ‘yan kwanakin nan.
Matsalar tsaro ta kara tabarbare a jihohin Filato da Benuwai, inda rahotanni ke cewa, wasu da ake zargin makiyaya ne daga kasashen waje ne ke kai hare-haren kashe rayuka da kuma raba al’umma da matsugunansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp