• English
  • Business News
Saturday, May 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Wutar Lantarki: Jihohin Kano, Katsina Da Jigawa Na Samun Wutar Awa 2 Ne Kacal A Kullum

by Sani Anwar
3 weeks ago
in Labarai
0
Kamfanin XD Na Kasar Sin Zai Gina Cibiyar Samar Da Lantarki A Sudan
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mazauna Jihohin Kano, Katsina da kuma Jigawa, na fuskantar mawuyacin hali, sakamakon katsewar wutar lantarki da kamfanin rarraba wutar lantarkin na Kano (KEDCO) ya yi.

Har ila yau, mazaunan sun bayyana cewa; a cikin kwanaki ukun da suka gabata, wutar sa’o’i biyu ko uku kacal suke iya samu a rana.

  • Muna Farin Ciki Da Karramawar Da Gwamna Abba Ke Samu Saboda Aiki Tukuru – Hon. Ibrahim
  • An Sako Malamin Kiristan Cocin Katolika Da Aka Sace A Kaduna

Haka nan ma, wasu kananan kamfanoni a jihohin, sun koka tare da bayyana cewa; suna fuskantar matsaloli wajen gudanar da ayyukansu na kasuwanci, sakamakon wannan karanci na wutar lantarki.

Binciken jaridar Daily Trust ya nuna cewa, masu sana’o’i kamar irin su Walda, Dinki, Cajin waya, masu sayar da Kankara da sauran makamantansu, su aka fi jefa wa cikin mawuyacin hali, sakamakon wannan karanci na wutar lantarki, domin kuwa wasu sun dauki tsawon kwanaki ma babu wutar lantarkin kwata-kwata a unguwannin da suke.

Kazalika, Hukumar ta KEDCO; ta nemi afuwa kan katsewar wutar lantarkin, musamman ganin yadda aka dora mata alhakin matsalar na rashin sake kyautata hanyoyi da kuma samar da kayan aiki, wadanda za su taimaka wajen gyara wutar yadda ya kamata.

Labarai Masu Nasaba

Mutum 3 Sun Rasu, Wasu Sun Jikkata Yayin Da Bama-bamai Suka Tashi A Hanyar Borno

Hukuma Ta Haramta Bikin Ranar Kauyawa A Kano

Haka zalika, mazauna jihohin da abin ya shafa, sun koka kan wasu abubuwan more rayuwa, kamar ruwan sha da sauran makamantansu.

Masu Sayar Da Ruwa Sun Kara Farashi A Kano

A Jihar Kano, wani mazaunin unguwar Hotoro ta Arewa, a Karamar Hukumar Nassarawa, Malam Gambo Muhammad, ya ce; ana sayar da kowacce jarka daya kan Naira 70, kafin samun wannan karancin wutar lantarki, wanda a halin yanzu kuma ake sayar da ita kan Naira 120.

“Muna wahalar samun ruwan sha da arha a wannan yanki namu, manyan hanyoyin samun ruwa a Kano su ne, ta hanyar rijiyoyin burtsatsai (Boreholes), sannan ana iya samun ruwan ne ta hanyar amfani da wutar lantarki.

Don haka, da zarar an ce babu wutar lantarki, dole ne masu sayar da ruwan su nemi wata hanya daban, wanda hakan zai sa dole sayar da ruwan ya yi tsada. Sannan, a inda babbar matsalar take shi ne, ba kowa ne zai iya amfani da inji wajen samar da ruwan ba, wanda hakan ke kara sanya wa a samu karancin ruwan matuka gaya a wasu wurare”, in ji shi.

A wasu wuraren, labari ya iske mu cewa; wasu tun karfe shida na safe suke fita neman masu sayar da ruwa, sannan su kuma masu sayar da ruwan na ikrarin cewa; a kan layin neman ruwan suka kwana, don kawai su samu ruwan da za su sayar a wannan rana.

An kuma bayyana cewa, kankarar da ake sayar da ita Naira 100, yanzu ta koma 200.

Me Yasa Aka Samu Matsalar Wutar Lantarki?

Da yake magana kan matsalar katsewar wutar lantarkin a jihar, babban jami’in sadarwa na KEDCO, Sani Bala Sani, a cikin wata sanarwa da ya bayar ranar Asabar, ya bayyana faruwar hakan ne kan kokarin da ake yi na sake sabunta kayan aiki na rarraba wutar lantarkin.

Yayin da yake bayar da hakuri, kan ci gaba da matsalar da ake fuskanta ta wutar lantarkin, Sani ya ce kamfanin na kan kokarin kawo karshen matsalar, wanda hakan ke bukatar lura wajen aikin da kuma tsaron Injiniyoyinsu.

“Muna neman gafara ga abokanan cinikayyarmu masu girma da kima a wajenmu, sakamakon raguwar wutar lantarki da aka samu a halin yanzu.

“Ku tuna cewa, mun samu ci gaba kwarai da gaske wajen inganta rarraba wutar lantarki, wanda sakamakon a bayyane yake, ana samun wutar na tsawon awanni, ba tare da katsewa ba, sannan muna amsa kokenku cikin gaggawa, muna kuma ba ku wutar daidai gwargwado.”

Mun dage wajen yin wadannan gyararraki ne, sakamakon ganin yadda lokaci na Damuna ke karatowa, wannan ne ya tilasta mana sake bunkasa hanyoyin samar da wutar, don gudun samun katsewarta.

“Muna matukar ba ku hakuri da dukkanin matsalolin da aka samu tare kuma da tabbatar muku da cewa; wutar za ta dawo kamar yadda aka saba da zarar an kammala aikin. Muna godiya da uzurin da kuka yi mana da kuma hakurin da kuka yi”, in ji Sani.

A Jihar Jigawa, mutane sun koma amfani da rijiyoyin da aka yi watsi da su don samun ruwa, sannan kuma an dakatar da wasu sana’o’i daban-daban da suka hada da Walda da sauran masu alaka da ita, sakamakon karancin wutar lantarki.

Har ila yau, an kuma gano cewa; karancin ya shafi farashin wasu kayayyaki kamar Man girki da Kankara da kuma cajin Waya, sakamakon yadda masu gudanar da aikin suka kara kudade, domin karin da su ma suka samu.

A cewar wani mai sana’ar sayar da ruwan, Sani Talle ya ce; kwana uku kenan ba su samu wutar lantarki a yankinsu ba, wannan dalili ne ya sa bai loda ruwa a motarsa ba, sakamakon karancin wutar lantarkin a fadin jihar. Ya kara da cewa, karancin wutar lantarkin, ya tilasta wa masu sayar da ruwa yin watsi da manyan motocinsu, tare da neman wasu hanyoyin da za su ciyar da kawunansu.

“Wutar awa biyu ko uku kacal suke bayarwa a rana, sannan kuma a nan Jigawa, hanyoyin samun ruwan su ne, rijiyar birtsatsai (boreholes), sannan za ka yi mamakin yadda cikin awa biyu kacal wutar lantarki ke jan ruwa zuwa wannan rijiya. Yanzu haka, kwana uku kenan ina zaune babu ruwan d azan sayar. Idan ka zaga yanzu, za ka ga yadda mutane suka koma amfani da ruwan rijiyar da a da suka yi watsi da ita”, in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, akwai da dama daga cikin masu irin sana’ar tasa da suke tunanin barin sana’ar su nemi wata, sakamakon irin wannan matsala da kan faru dangane da wutar lantarki.

Har ila yau, tattaunawa ta barke a shafukan sada zumunta na Nijeriya, inda ake yin korafin cewa; sai tsawon wane lokaci KEDCO, za ta yi magana kan wannan matsala ta rashin wutar lantarki.

Da yake mayarwa da kamfanin KEDCO martani a shafinta na Twitter (D), Abdulmalik Attah ya bayyana uzurin da kamfanin ya bayar a matsayin ‘labara’ kawai, inda ya kara da cewa; hakan na nufin ba za a samu wutar lantarki ba, har nan da zuwa tsawon mako uku, idan aikin ya ɗauki tsawon wannan lokaci.

Wani shi ma, mai amfani da shafin na sada zumunta (D), Muhammad Madaka ya ce, sanarwar da kamfanin ya bayar, a makare ta zo, wadda kusan ana iya cewa; ba ta da wani amfani.

“Sai bayan kun ji mutane suna ta faman korafi ne, sannan kuka yanke shawarar kawo wannan uzuri na sanarwa, babu wani lokaci da ake da yakini wannan aiki naku zai kammalu.”

Rabiu Adam, wanda ya yi wa hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC) sharhinsa, ya yi zargin cewa KEDCO na bai wa Kani fifiko, sakamakon yadda Katsina ke shan wahala a hannunta (KEDCO).

“Ko ma’aikatan KEDCO da ke Jihar Katsina, ba su san dalilin katsewar wutar lantarkin ba, kusan mako guda kenan babu wutar, don haka batun cewa; ba wata babbar matsala ba ce, rainin wayo kawai.”

An Rufe Matsakaita Da Kananan Kamfanonin A Jihar Katsina

Haka ma al’amarin yake a Jihar Katsina, yayin da mazauna yankin suka yi ikrarin cewa; ba sa samun wutar da ta wuce awanni uku a rana. Kazalika, sun kuma bayyana yadda kamfanoni ke rufewa, sakamakon wannan matsala ta katsewar wutar lantarkin.

Hukumar Kula Da Wutar Lantarki Ta Kasa Ta Ci Tarar Kamfanonin Rarraba Wutar Lantar Takwas

Wannan dai, na zuwa ne mako biyu bayan Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC), ta sanar da cin tarar wasu Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarkin (DisCos), su kimanin takwas Naira miliyan 628,031,583.94, sakamakon karya dokar da ta sanya a kan kudin da aka kiyasta ga kwastomomin da ba a tantance ba.

A cewar Hukumar ta NERC, kamfanonin da suka hada da KEDCO, an ci tarar su ne bisa ga sashe na 34(1)(d) cikin baka, na dokar samar da wutar lantarki ta 2023 da kuma rashin cika ka’idojin da hukumar ta fitar a tsakanin watan Yuli da kuma na Satumbar 2024.

Sauran, sun hada da Hukumomin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja, Iko, Inugu, Ikeja, Jos, Kaduna da kuma Yola.

Fadar Shugaban Kasa Na Shirin Kashe Naira Biliyan 10 Don Sama Wa Kanta Wutar Lantarki

A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke fama da matsalar wutar lantarki, fadar shugaban kasa na shirin kashe Naira biliyan 10 wajen samar da wuta ga fadar shugaban kasar.

Kamar yadda aka samu lamuni a 2025, aikin samar da wutar lantarkin da aka yi wa lakabi da “Samar da wutar lantarki ta hanyar na’ura mai amfani da hasken rana a fadar shugaban kasa”, wanda aka ware wa Naira biliyan 10 a cikin kasafin kudin da za a batar ayyukan fadar ta shugaban kasa.

Matakin na zuwa ne daidai lokacin da ake kara nuna damuna kan rashin tabbacin wutar lantarki da kuma tsadar wutar kan daidaikun al’ummar wannan kasa da kuma sauran cibiyoyin gwamnati.

Ana sa ran aikin samar da hasken wutar zai rage dogaro ga tsarin samar da wutar lantarki na kasa tare kuma da takaita tasirin karin kudin fiton, kan kudaden gwamnati.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: JigawakanoKatsinaKedcoMatsalaWutar Lantarki
ShareTweetSendShare
Previous Post

Muna Farin Ciki Da Karramawar Da Gwamna Abba Ke Samu Saboda Aiki Tukuru – Hon. Ibrahim

Next Post

An Bude Taron Dandalin Tattaunawar Afirka Ta Yamma Karo Na Farko A Senegal

Related

Boko Haram Sun Kashe Mutum 12 A Wani Sabon Hari A Borno
Manyan Labarai

Mutum 3 Sun Rasu, Wasu Sun Jikkata Yayin Da Bama-bamai Suka Tashi A Hanyar Borno

4 hours ago
Hukuma Ta Haramta Bikin Ranar Kauyawa A Kano
Labarai

Hukuma Ta Haramta Bikin Ranar Kauyawa A Kano

6 hours ago
Dalilin Ƴansandan Kano Na Tsare Wasu Awaki
Labarai

Dalilin Ƴansandan Kano Na Tsare Wasu Awaki

8 hours ago
Ƙungiyar Fulani Makiyaya Ta Nuna Damuwarta Na Ɓacewar Mataimakin Shugabanta
Labarai

Ƙungiyar Fulani Makiyaya Ta Nuna Damuwarta Na Ɓacewar Mataimakin Shugabanta

8 hours ago
Hisbah Ta Rufe Otal, Ta Kwato Ƙwalaben Giya 209 A Yobe
Labarai

Hisbah Ta Rufe Otal, Ta Kwato Ƙwalaben Giya 209 A Yobe

10 hours ago
Babu Wani Dan Jarida Da Aka Hana Shiga Taron Gwamnonin Arewa – CPS Ibrahim Musa
Labarai

Babu Wani Dan Jarida Da Aka Hana Shiga Taron Gwamnonin Arewa – CPS Ibrahim Musa

10 hours ago
Next Post
An Bude Taron Dandalin Tattaunawar Afirka Ta Yamma Karo Na Farko A Senegal

An Bude Taron Dandalin Tattaunawar Afirka Ta Yamma Karo Na Farko A Senegal

LABARAI MASU NASABA

Crystal Palace Ta Lashe Kofin FA Karon Farko, Ta Doke Manchester City 1-0

Crystal Palace Ta Lashe Kofin FA Karon Farko, Ta Doke Manchester City 1-0

May 17, 2025
Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

May 17, 2025
Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taro Na 34 Na Kasashen Larabawa

Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taro Na 34 Na Kasashen Larabawa

May 17, 2025
Jami’ar FUDMA Ta Ƙara Fadawa Cikin Rikicin Shuagabanci A Katsina

Jami’ar FUDMA Ta Ƙara Fadawa Cikin Rikicin Shuagabanci A Katsina

May 17, 2025
Rokar Kasuwanci Ta Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 6 Zuwa Sararin Samaniya

Rokar Kasuwanci Ta Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 6 Zuwa Sararin Samaniya

May 17, 2025
Gidan Adana Kayayyakin Tarihi Na Amurka Ya Mayarwa Kasar Sin Rubuce-rubucen Hannu Masu Daraja Na Lokacin Yake-yake A Kasar

Gidan Adana Kayayyakin Tarihi Na Amurka Ya Mayarwa Kasar Sin Rubuce-rubucen Hannu Masu Daraja Na Lokacin Yake-yake A Kasar

May 17, 2025
Bude Kofar Kasar Sin Dama Ce Ga Duniya Har Abada

Bude Kofar Kasar Sin Dama Ce Ga Duniya Har Abada

May 17, 2025
Boko Haram Sun Kashe Mutum 12 A Wani Sabon Hari A Borno

Mutum 3 Sun Rasu, Wasu Sun Jikkata Yayin Da Bama-bamai Suka Tashi A Hanyar Borno

May 17, 2025
Hukuma Ta Haramta Bikin Ranar Kauyawa A Kano

Hukuma Ta Haramta Bikin Ranar Kauyawa A Kano

May 17, 2025
Dalilin Ƴansandan Kano Na Tsare Wasu Awaki

Dalilin Ƴansandan Kano Na Tsare Wasu Awaki

May 17, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.