Shugaban Æ™ungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF), kuma gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya jagoranci takwarorinsa wajen ziyarar ta’aziyyar ga mataimakin shugaban Æ™asa, Kashim Shettima, bayan dawowarsa birnin tarayya Abuja, a ranar Laraba.
Gwamnonin, sun yi addu’ar Allah ya jiƙan surukar mataimakin shugaban ƙasa, marigayiya Hajiya Maryam Albishir, ya kuma bai wa iyalanta haƙurin jure rashinta.
- Nijeriya Ta Aike Dakaru 177 Guinea Bissau Don Wanzar Da Zaman Lafiya
- Philippines Ta Zama Makamin Sarrafawa Ga Amurka
Da yake godiya da ziyarar, mataimakin shugaban Æ™asar, ya nuna jin daÉ—insa kan ta’aziyar da gwamnonin suka kawo da yadda suka nuna tausayi da goyon baya gare shi.
Shettima ya yaba da haɗin kan Gwamnonin da Gwamnatin Tarayya ya kuma yi kira da a ƙara ba da hadin kai da goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu, domin cimma manufofinsa da na ƙasa baki daya.