Yayin da ake cika wasu shekaru fiye da 10 da raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin Sin da Australia, firaministan kasar Australia Anthony Albanese, yana ziyara a kasar Sin tun daga ranar 12 zuwa 18 ga wannan wata, ziyarar da ta jawo hankalin kafofin watsa labaru na kasa da kasa.
Hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya suna daga cikin manyan batutuwan da firaminista Albanese ya mai da hankali kansu a yayin ziyararsa ta wannan karo. Ya kuma jagoranci wata tawagar manyan shugabannin kamfanonin kasar Australia zuwa kasar Sin, kana ya tabbatar da cewa kasarsa ba ta taba neman yanke hulda da kasar Sin ba a fannin tattalin arziki.
A shekaru 10 da suka gabata, kasashen Sin da Australia sun sa hannu kan yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci ta wata hanya mai inganci, wadda ta sa kaimi ga hadin gwiwarsu, musamman a fannin harkokin raya tattalin arziki da cinikayya. A halin yanzu kuma, kasar Sin ta kasance abokiyar hulda ta fannin cinikayya mafi muhimmanci, kuma babbar kasuwar shige da fice ga kasar Australia. A wannan karo, kasashen biyu suna maraba da yin tantancewa, da tattaunawa kan yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci, don tabbatar da kyautata da fadada fannonin hadin gwiwarsu.
An lura cewa, kasashen Sin da Australia za su kara yin hadin gwiwa a fannonin gargajiya, kamarsu aikin noma da hakar ma’addinai, da kokarin fadada sabbin fannonin hadin gwiwarsu, kamar fasahar AI, da kiwon lafiya, da makamashi mai tsabta, da tattalin arziki ta yanar gizo da sauransu, don sa kaimi ga daga matsayin hadin gwiwarsu zuwa wani sabon mataki. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp