Kafafen yada labarai na kasar nan, na ci gaba da ganin tasku, saboda yadda a kasar, ake ci gaba da fuskantar matsin halin rayuwa.
Wannnan kalubalen har ta kai ga shafar masu kafafen yada labarai a kasar, idan aka yi la’akari yadda suke ta hakilon fadi tashi, saboda tashin Gwauron Zabin kayan da suke gudanar da aikinsu, musamman ma ta vangaren kamfanonin jaridu, da tsadar kayan aikin ke sanya su gaza iya sayen kamarsu takardar wallafa Jarida, Tawada.
Suma kafafen Talabijin da Radiyo, suna fuskantar tsadar kayan aikin gudanar da shirye- shiryensu, inda yanayin da kafafen yada labarai a kasar suke a cikin yanzu, na matsin tattalin arziki, ke kara munana matuka fiye da yadda ake tsammani lamarin.
- Yadda LEADERSHIP Da Gwamnatin Nasarawa Suka Jagoranci Horas Da Matasa 100 San’o’in Dogaro Da Kai
- Jiragen NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Tare Da Tarwatsa Ma’ajiyar Abincinsu A Tafkin Chadi
Kazalika, masu kafafen yada labaran na ci gaba da kokarin tafiyar da ayyukansu ne, a cikin yanayin da ake ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kaya, da hauhawar kudaden musanya da kuma tsadar kayan gudanar da aiki. Saboda matsalar kudaden musanyar, hakan yayi sanadiyar zubar da darajar Naira da kuma tsadar kayan tafiyar da kafafen na yada labarai ke ci gaba da fuskanta.
A Nijeriya, kafafen sun kasance suna daya daga cikin fannonin da ke taimakawa wajen kara bunkasa
tattalin arzikin kasar. Sai dai kuma kash! Saboda ci gaba da fuskantar wannan kalubalen na matsin tattalin azrkin tare da tsadar kayan aikin, tafiyar da kafafen yada labaran, na neman gagarar su.
Batun da aka mayar da kai wajen tattaunawa a taron kwana uku da kungiyar Editoci ta kasa (ANEC), wanda ya gudana a Yenagoa , babban birnin jihar Bayelsa, wanda ya samu halartar masu kafafen yada labarai da kungiyar Editoci (NGE), mahalarta taron sun bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta samar masu kafafen dauki, musamman ma la’akari da yadda illar cire tallafin mai da ta yi, wanda cirewar ce ta shafi kafafen yada labaran kasar da kuma yadda ake musanyar kudaden hakan ke kara jefe su, a cikin matsala. Kazalika, sun yi kira ga gwamnatin da ta samar masu da tallafi ko kuma ta samar masu da sauki a kan biyan haraji, domin ci gaba da fuskantar kalubalen matsin tattalin arzki, wani lamari ne da zai kara jefa ayyukansu cikin rashin tabbas wajen dorewar ci gaban aiwatar da ayyukan wasu daga cikinsu.
A cikin jawabin bayan taro da shugaban kungiyar NGE na kasa Eze Anaba ya sawa hannu tare da Sakatarenta Dakta Iyobosa Uwugiaren, sun yi dubi a kan alfanun matakan dogon zango na sauye-sauyen da gwamnatin ta kirkiro da su, sai dai, sun yi nuni da cewa, wadannan sauye-sauyen kafofin ba za su iya ci gaba da jure masu ba, musamman kalubalen da suke ci gaba da fuskanta na gudanar da ayyukansu.
Bugu da kari, sun bakaci gwamnatin da samar wa kafafen kyakyawan yanayi, ta hanyar yin nazari a kan tsare-tsaren harajin a kan kayan da suke saye, domin tafiyar da kafofin. Daya daga cikin manyan kalubalen da, musamman kafafonin jaridu a kasar suke ci gaba da fuskanta shi ne, tsadar takardun buga jaridun da a turance ake kira da Roll, inda farashinsu, ke ci gaba dayin tashin Gwauron Zabi, duba da yadda ake sayar da tan din takardar, a kan Naira miliyan biyu.
Wannan tsadar dai, ta janyo wasu kamfanonin buga jaridun a rage yawan shafin da suke wallafa labaran su, wanda hakan ya tilasata su, kara farashin jaridun da suke sayarwa. Kazalika, Tawadar da ake buga jaridun, ita ma farashin ta, ya karu, wanda hakan ya kara zamowa kafanonin jaridun, wani babban kalubale, duba da yadda suke kashe dimbin kudade, kafin su iya buga jaridun.
Ta gefe daya kuma, kafafen yada labarai na Talabijin da Radiyo, kayayyakin aikinsu, sun yi tsada, wanda hakan ya sa suka gaza sayen kayan aiki na zamani don gudanar da ingantacen aiki. Yawan samun hauhawar kudaden musanya na waje da ya janyo karyewar darajar Naira tare da cire tattalafin mai, hakan ya kara zamowa kafafen yada labaran babbar koma baya ne, wajen gudanar da ayyukansu.
Bugu da kari, karyewar darajar Naira, hakan ya zamewa kamafanonin jaridun matukar tsada, wajen iya shigo da takardun buga jaridun ko kuma sayen Tawadar buga jaridun, inda hakan suma kafafen Talabijin da Radiyo, ke kashe dimbin kudade, musanya wajen shigo da na’urorin tafiyar da
kafafensu.
Ya zama wajbi gwamnatin ta dauki matakan gaggawa domin ta magance wa kafofin wannan dimbin kalubalen da suke ci gaba da fuskanta, musamman ta hanyar samar masu da wani rangwame a kan tsadar kayan aikin da kuma rage masu bashi mai saukin ruwa domin su zuba jari a fannin.
Ta wannan hanyar ce kawai, kafafen za su iya ficewa daga cikin wannan kangin na matsain tattalin arzikin da suka ci gaba da fuskanta, wanda idan suka fice daga cikin kangin, za su samu sukunin ci gaba da bayar da gudunmawar su, wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
Kundin tsarin mulkin Nijeriya dai, ya bai wa kafafen yada labarai ‘yancin sanya ido a kan yadda gwamnatin kasar ke tafiyar da shugabancin ta, musamman ma idan aka yi la’akari da sashe na 24 na kudin tsarin mulkin. Sai dai, abin takaici, har yanzu saboda irin wadannan kalubalen sun tauye karsashin kafofin wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, inda wadannan kalubalen, suka sanya su ke kai gwauro da mari, don su ci gaba da rayuwa.
Duba da yadda kafafen ke taka muhimmiyar rawa wajen gina kasa, hanyar gudanar da ayyukansu, bai kamata ace gwamnatin ta barsu suna ci gaba da fuskantar wadannan kalubalen ba.
Ra’ayinmu a nan shi ne, barinsu a cikin wannan yanayi, zai dakushe kokarinsu kan gudunmawar da suke ci gaba da bayar wa, wajen fadakarwa, ilimantar da kuma nishadantar da al’ummar kasar.