ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, November 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Ƙabilanci Da Saɓanin Makiyaya Da Manoma Ya Zama Tarihi A Jihar Kaduna – KSPC

by Sulaiman and Shehu Yahaya
10 months ago
Kaduna

Hukumar wanzar da zaman lafiya ta Jihar Kaduna ( Kaduna State Peace Commission ) Ta bayyana cewa, matsalar rikice-rikicen Ƙabilanci da na Fulani Makiyaya da Manoma yanzu ya zama tarihi a faɗin jihar baki ɗaya.

Muƙaddashiyar Mataimakiyar Shugabar Hukumar, Hajiya Khadija Hawaja Gambo ce ta tabbatar da hakan yayin taron bita akan ayyukan hukumar na shekaru biyar da suka gabata tare da wasu kungiyoyin wanzar da zaman lafiya a jihar Kaduna,  wanda ya gudana a ɗakin taro na gidan Hassan Usman Katsina da ke Kaduna.

ADVERTISEMENT
  • Sin A Shirye Take Ta Shawo Kan Sabani Tare Da Sabuwar Gwamnatin Amurka
  • Jami’o’in Sin Da Najeriya Sun Yi Kira Da A Yaukaka Fahimta Tsakanin Al’adun Kasashe Masu Tasowa

Hajiya Gambo, ta ce “Yau fiye da Shekaru Biyar ba a samu matsalar ɓarkewar rikice-rikicen kabilanci ko Fulani makiyaya da manoma ba, wanda hakan ya furu ne bisa jajircewar hukumarmu wajen samun haɗin kan ɗaukacin al’ummar jihar Kaduna.

LABARAI MASU NASABA

’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi

Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

“Nasan yanzu an manta shekarar da aka samu rikicin kabilanci ko Fulani makiyaya da manoma a kaduna kuma idan babu hadin kan mutane, ba za mu samu wannan nasarar ba, wannan yana nuna cewa kowa yana da rawar takawa, ba wai kawai nauyi ne da ya rataya akan hukumarmu ba har da ma hada hannu da shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki wajen samar da tsare-tsaren wanzar da zaman lafiya. Muna aiki ba dare ba rana don neman zaman lafiya ya dore acikin al’ummar jiharmu”.

“Don haka, a yanzu Kaduna duk wani rikicin kabilanci ya zama tarihi, muna fata, jihar Kaduna ta zama abin koyi ga sauran jihohin da ke fama da irin wannan matsalar, su samu ilimin yadda muka yi muka warware namu matsalar, saboda haka, mu kullum a shirye muke wajen tabbatar da cewa an samu hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummarmu baki daya”.

A nata jawabin, babbar Daraktar kungiyar wayar da kan mata ta jihar Kaduna, Misis Hannatu Aruwan, ta bayyana gamsuwarta dangane da matakan da hukumar wanzar da zaman lafiya ta jihar Kadauna ke aiwatarwa wajen kara hada kan daukacin alummar jihar.

Akan hakan, Hannatu Aruwan ta bukaci gwamnatin jihar Kaduna da ta kara tallafa wa hukumar da kudade wajen ci gaba da kokarinta na wanzar da zaman lafiya da hadin kan al’umma wajen warware duk wata matsala da ke barazana ga wanzar da zaman lafiya a jihar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bukatar Samar Da Cikkakken Tsaro Ga Hukumar Zabe
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi

November 18, 2025
Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas
Labarai

Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

November 17, 2025
NBS
Labarai

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%

November 17, 2025
Next Post
Nijeriya Ta Yaba wa Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Gaza

Nijeriya Ta Yaba wa Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Gaza

LABARAI MASU NASABA

Bukatar Samar Da Cikkakken Tsaro Ga Hukumar Zabe

’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi

November 18, 2025
Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

November 17, 2025
Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

November 17, 2025
An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

November 17, 2025
NBS

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%

November 17, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

November 17, 2025
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

November 17, 2025
Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

November 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.