Kantoma na karamar hukumar Takum ta Jihar Taraba, Hon. Boyi Manja, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar sabida barkewar rikicin addini.
Rikicin addini ya barke a karamar hukumar Takum a ranar Lahadin da ta gabata tsakanin musulmi da kiristoci yayin da wasu ‘yan bindiga sanye da kakin ‘yan banga suka kashe mutum biyu a Rafa Kasuwan Shanu daura da hanyar Wukari a cikin garin Takum.
Manja yayin da yake zantawa da LEADERSHIP ya tabbatar da cewa ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 domin kaucewa ci gaba da kashe-kashe da lalata dukiyoyi a yankin.
LEADERSHIP ta tattaro cewa akalla mutane shida ne suka mutu a rikicin yayin da aka lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.