Shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da tawaga zuwa jamhuriyar Nijar a kokarin kungiyar na neman mafita mafi sauki don wanzar da zaman lafiya a kasar cikin gaggawa.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Alhamis, matakin ya yi daidai da kudurin da aka cimma a karshen babban taron kungiyar ECOWAS da aka gudanar a karshen makon da ya gabata a Abuja.
Tawagar, karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) ta tashi zuwa birnin Yamai ne a ranar Alhamis bayan ganawa da shugaba Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja.
Tawagar ta hada da mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III da shugaban hukumar ECOWAS H.E. Umar Aliyu Touray.
Shugaban ya kuma aike da wata tawaga ta daban karkashin jagorancin Ambasada Babagana Kingibe domin tattaunawa da shugabannin kasashen Libya da Aljeriya duk kan rikicin da juyin mulkin Nijar ke shirin haifarwa.
Da yake jawabi ga tawagogin biyu, shugaba Tinubu ya bukace su da su yi amfani da hikima da basirarsu don yin duk abin da ya kamata don ganin an cimma matsaya mai kyau da kwanciyar hankali a Nijar domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Afirka maimakon wani yunkuri na tarzoma irin yadda sauran wasu yankunan Duniya suke yi.