Rikicin wurin aiki tsakanin wasu ma’aikata biyu ya rincabe yayin da ɗaya ya rasa ransa sakamakon rikicin a ranar Lahadi, 21 ga watan Janairu, 2024.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, rikicin ya faru ne a Kamfanin ‘Fas Agro Sacks’ da ke Sharada Ja’in Quarters a Jihar Kano, Inda James Isma’il ya yi sandin mutuwar Mohammad Tukur Adamu mai shekaru 32 a duniya.
- An Samu Hauhawar Farashi Mafi Muni A Nijeriya
- ‘Yan sanda Sun Cafke Waɗanda Ake Zargi Da Satar Mutane A Abuja
Rikicin dai ya samo asali ne daga rashin jituwa yayin gudanar da ayyukansu na kamfanin, sa’o’i kadan bayan kammala ayyukansu, suka fara rigimar da ta yi sanadin rasuwar a harabar kamfanin.
Bayan haka ne wasu gungun ‘yan daba suka yi amfani da wannan damar suka fara satar dukiyar jama’a tare da yunkurin cinnawa kamfanin ‘Fas Agro Sacks’ wuta amma Hukumomin tsaro sun kwantar da tarzomar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kano (PPRO), SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na Facebook.
Sanarwar ta bayyana cewa, an kai Tukur Adamu asibitin kwararru na Murtala Mohammed, inda wani kwararren likita ya tabbatar da rasuwarsa. An kama James Isma’il, wanda ake zargi da aikata laifin, tare da wasu mutane 13 da ake zargi da tayar da tarzoma.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, ya baiwa mazauna yankin tabbacin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.