Ganin yadda al’umma suke radain aka dalilan da suka aka dakatar da akin hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma yadda ake halin ake yada cewa an kwace kwangilar aikin daga hannun kamfanin Julius Berger wadda take aikin, wai kuma na mika wa kamfanin Dangote da BUA.
A kan haka ne Mukaddashin Editanmu Bello Hamza ya tattauna da mataimaki na musamman a bangaren harkar yada labarai ga Ministan Ayyuka Sanata Dabid Umahi, wato Hon. Barsita Orji Uchenna Orji, inda ya warware zare da abawa a kan yadda lamarin yake da halin da ke ciki a yanzu.
- Abin Da Ya Sa Ƙasashen Duniya Suka Gina Majalisar Ɗinkin Duniya – Sakatare Janar
- Xi Ya Halarci Taron Tattaunawa Na Jagororin “BRICS+” Tare Da Gabatar Da Muhimmin Jawabi
Akwai labari da yake yawo cewa gwamnati ta kwace kwangilar aikin titin da ta bai wa kamfanin Julius Berger na hanyar titin Abuja zuwa Kaduna shekara 6 da suka wuce, cewa an bai wa wasu kamfanoni daban-daban?
Ba gaskiya ba ne, yadda abin yake shi ne gwamnatin tarayya ta amince da wasu kudaden da ba zan iya kididdige su ba a kan kamfanin Julius Berger na aikin da ta kammala. Ka san an raba abin bangare-bangare ne. Akwai na kamfanin Julius Berger akwai na kamfanin Dangote dayan kuma na BUA. An sake duba na kamfanin Julius Berger a kan kudaden da duba da yanayin yadda kasa ke ciki. Amma sai suka ce duk da sabon nazarin da gwamnatin tarayya ta yi su ba za su yi ba sai dai an kara masu kudi. Amma yanzu duk da rokon da muka bas u amince da ci gaba da aiki ba. Saboda da ba za a dinga mu’amala da kamfanin Julius Berger kamar yadda ake mu’amala da sauran kamfanonin kasar nan. An sake nazari a kan aikin wanda gwamnati kuma ta yarda dashi yanzu kuma su dawo suce suna son kari babu adalci a ciki kuma halin ko’in kula ne.
Babban Ministan ayyuka na kasa wanda muka san cewa mutum ne wanda ya san darajar kudi kuma yana girmama aiki mai kyau da inganci. Ministan ya ce, su koma su ci gaba da aiki duba da amincewar da gwamnati ta yi. Kada su dawo suna tambayar wasu kudade kuma a irin wannan lokaci. Wannan ya zama kamar ba a yi wa gwamnati adalci ba. Gwamnatin Nijeriya ta dade tana mu’amala da kamfanin Julius Berger tsawon shekaru. Kuma ba wai sun fi kowa ba ne. Saboda ba zai yiwu sufi kowa ba. Abin da minista yake cewa shi ne su koma aiki. Wannan shi ne abin da Minista ya ce masu. Yanzu ma’akatar Ayyuka ta sake duna kwangilar ne da nufin kasa ta amfana. Wannan shi ne matsayarmu. Kuma wajen sake bibiyar kwantragin akwai hanyoyi da dama da ake bi. Ba za a dinga mu’amala da kamfanin Julius Berger kamar saniyar ware ba. Sauran ma’aikata sun koma aiki. Muna fatan kamfanin Julius Berger za su yi tunani a kai su yi abin da ya dace. Amma kuma su sani cewa shi Minista Dabe Umahi mutum ne tsayayye kuma bashi da tsoro. Zai yi abin da ya dace idan suka ki komawa bakin aiki. Wannan lokaci da mutane, kamfanoni da sauran ‘yan kasuwa ya kamata su sani cewa wannan lokacin sadaukarwa ne. Dole ne mu sadaukar domin ci gaban wannan kasar. Kamar yadda sauran kasashe suke ciki wannan lokaci ne na matsin tattalin arziki da take bukatar kowa ya sadaukar. Sun yi tunanin kamar yadda a ka saba ne. Amma wannan shugaban ma’aikatan ayyukan ya tabbatar da cewa dole kowa ya yi abin yadda ya kamata. Dole a dinga bin diddigi kuma mu saka Nijeriya a gaba a duk abin da muke yi. Wasu lokutan ba za ka samu riba duka ba. Abin da yake da amfani shi ne yin aikin. Manyan ayyuka da gine-gine babban abu ne a wajen yi wa mutane hidima.
Wannan Jaridar Hausa ce, kuma mafi yawan masu karanta Jaridar ‘yan Arewa ne, akwai zantuka da suke yawo cewa shi Babban Minista Dabe Umahi bai damu da wannan hanyar ta Abuja zuwa Kaduna ba kuma gashi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Ina so ka yi bayani saboda a tausasa zukatan wadannan mutanen cewa shi Minista mutum ne da ya saka duka mutanen kasa a zuciyarsa ba tare ka bambanci ba.
Wadannan zantuka basu da tushe kuma ba a yi su ma da kyakkyawar niyya ba. Shi mutum ne da a ka sani a matsayin mai hadin kai. Mutum ne dan Nijeriya. Ayyukansa a matsayin Gwamna ya nuna haka. Mai girma Minista, ina tabbatar maku da cewa abu na farko da ya fara yi shi ne aikin Abuja, Kaduna, Zaria. Ya nace a kan cewa za a yi aiki mai karko. Saboda haka ne a ka raba aiki gida uku a yanzu. Saboda a yi shi da sauri kuma mai karko. Wani sashe kanfanin BUA yake yi. Wani sashen kamfanin Dangote. Ana sa ran aikin zai yi karkon shekara hamsim. Zan iya tabbatar maka da cewa aikin idan an gama shi zai zama cikin wanda suka fi kyau a Nijeriya. Wannan aikin na daga cikin ayyukan ‘Renewed Hope Agenda’ saboda wannan hanyar na daya daga cikin manyan hanyoyi a Nijeriya. Yana da muhimmanci a fannin kasuwanci. Ina tabbatar maka da cewa babbar ma’akatar ayyuka ta maida hankali a kan wannan hanya domin a gama aikin a kan lokaci. Sauran ‘yan arewa kuma ina tabbatar masu da cewa Babban Ministan na nan a kan ‘Renewed Hope Agenda’ na shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma mutum ne wanda yake aiki bisa daidaito tsakanin duka bangarorin kasar. Ina tabbatar maku da cewa muna yin haka. Kuma duk manyan ayyukan da mai girma shugaban kasa wanda a ka fito dasu karkashin wannan gwamnati, Arewa da kudu suna da ayyuka masu tsawo dai-dai. Wannan na nuna cewa shi Babban Minista na aiki da abubuwan da shugaban kasa ya bukata. Arewa maso yamma, yanki da yake da muhimmanci musamman bangaren noma da sauran abubuwa duk wanda yake son tsayayye da kuna wadataccen abinci dole ya zo Arewa. Ina tabbatar maka da cewa wannan gwamnati tana sane da wannan kuma tana yin duk abin da ya dace domin tabbatar da cewa hanyoyin arewa an kula dasu yadda ya kamata.
Sannan kuma hanyoyin da ke kudu suma haka. Ina fada maka cewa hanyar Sakwato –Badagry babban aiki ne muka sa a gaba. Wanda zai kara cigaba don bunkasa bangaren noma da sauransu. Kuma zai kawo ci gaba wajen mu’amala a tsakanin yankuna. Bana so in riga Malam masallaci, amma a kasa da awa arba’in da takwas Minista Umahi zai ziyarci Jihar Kebbi da Sakwatto domin kaddamar da ayyukan ‘Renewed Hope Agenda. Ina tabbata maka da aikin zai mai kimanin kilomita dubu. Jihar Sakwatto za ta amfana. Kebbi ma za ta anfana. Tare da sauran jihohi. Harda Jihar Neja duk a arewa. Ina kara tabbatar maka da cewa muna kuma da aikin Babbar hanyar Kros Ribas, Kogi, Binuwai, Nassarawa da Abuja wannan ma yana cikin aikin Renewed Hope Agenda na wannan lokacin. Kuma muna da aikin Akwannga – Jos. Wadannan ayyuka ne da aka kaddamar kari a kan wadanda gwamnatin baya ta kaddamar. Saboda da haka, ba siyasa za a yi ba. Shugaban kasar Nijeriya mutum ne na kowa da kowa. Kuma mai kaunar dimokuradiyya. Abin da ya yi shi ne ya fito fili a wajen ayyukan shi domin ganin cewa an gano tushen tattalin arziki. Ta hanyar tabbatar ayyukan da za su kawo ci gaba kuma su tabbatar da kasuwanci da noma da sauransu. Kuma arewa za ta amfana da wannan wajen habbaka tattalin arziki a Nijeriya.