A safiyar yau ne, kasar Sin ta yi amfani da rokar Long March-2D wajen harba rukunin taurorin dan Adam zuwa sararin samaniya, wanda ya nuna nasarar da kasar ta cimma wajen amfani da rokar wajen harba kumbuna sau 103 a jere.
Nasarorin da aka cimma a baya wajen amfani da rokar ta Long March a jere shi ne 102, wanda aka fara cimmawa daga shekara 1996 zuwa ta 2011.
Tun daga ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2020, rukunin rokar Long March na kasar Sin, ya cimma nasarori 103 a jere a cikin watanni 27 kacal, inda ya yi jigilar sama da kumbuna fiye da 200 zuwa sararin samaniya, ciki har da na’urorin binciken tashar sararin samaniya, da na binciken duniyar wata, da duniyar Mars, da kuma kumbo mai dauke da ‘yan sama jannati.
Kamar yadda hukumar binciken kimiyya da fasahar sararin samaniyar kasar ta bayyana.
Hukumar ta kara da cewa, kasar Sin na kera na’urorin harba kumbuna da manyan rokoki, wadanda za su yi jigilar ma’aikata zuwa duniyar wata a nan gaba, da kara yin balaguro zuwa duniyar Mars, da Jupiter da sauran kananan duniyoyi da ake kira asteroids. (Ibrahim)