Shahararrun yan wasan da suka canza sheka zuwa wasu kungiyoyin lararabawa a bana da suka hada da Neymar, Benzema da kuma Cristiano Ronaldo na fatan ganin sun lashe kofin zakarun Asia.
Neymar wanda ya koma Al-Hilal a watan Agusta ya fara buga gasar lig a ranar Juma’a yayin da kungiyarsa ta Al Hilal kuma zakarun Asia har sau hudu ta lallasa Abha da ci 6-1.
- Neymar Ya Fara Wasansa Na Farko A Al Hilal Da Kafar Dama
- Ronaldo Ba Zai Buga Wasa A Karawar Da Za Su Yi Da Kasar Luxembourg Ba
A daya bangaren kuma Ronaldo zai jagoranci Al-Nassr zuwa Tehran a ranar Talata domin karawa da Persepolis.
Cristiano Ronaldo, Neymar da Karim Benzema sun lashe gasar cin kofin zakarun Turai a hade guda 11, kuma daga ranar litinin za su jagoranci kungiyoyin gasar Saudi Arabia a gasar cin kofin nahiyar Asiya.
A bana dai kungiyoyin na Saudiyya sun kashe kusan dala miliyan 950 wajen sayen wasu manyan taurari a duniya.
An kashe kudaden ne sakamakon asusun saka hannun jari na masarautar Saudiya ya yi na karbar hannun jari mai rinjaye a manyan kungiyoyi hudu na kasar, Al-Hilal, Al-Ittihad, Al-Ahli da Al-Nassr.