Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu a wasan da Portugal ta lallasa Bosnia-Herzegovina a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai na 2024.
Dan wasan mai shekaru 38, ya zura kwallo a ragar Bosnia da bugun fanariti kafin ya zura kwallonsa ta biyu a wasan wadda kuma itace ta 127 da ya ci wa kasarsa Portugal a dukkan kwallayyen da ya buga mata a tarihi.
- Yadda Nijeriya Ta Yi Nasara A Wasan Sada Zumunci Da Mozambique
- Me Yake Faruwa Da Kungiyar Brighton A Kakar Bana?
Kasar Portugal, ta zira kwallaye biyar kafin a tafi hutun rabin lokaci, yayin da Bruno Fernandes, Joao Cancelo da Joao Felix suma suka zura kwallo a raga.
Sakamakon yana nufin Portugal ta kasance a saman rukunin J inda ta samu nasarori dari bisa dadari.
Ta zura kwallaye 32 kuma sau biyu kacal aka jefa mata kwallo a wasanni takwas da ta buga kawo yanzu, Ronaldo ya zura kwallaye tara a wasanni bakwai da ya buga.