Adadin wadanda suka mutu a wani bene mai hawa uku da ya rufta a unguwar Ojodu Berger da ke Legas ya kai biyar.
A cewar hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA), an ceto mutane 20 daga baraguzan ginin da ya ruguje.
- Tsarin BRICS Ya Zama Muhimmin Dandalin Hadin Kai Na Kasashe Masu Tasowa
- KOFIN DUNIYA: Za A Kara Yawan Kasashen Da Suke Bugawa Zuwa 64 A Shekarar 2030
Ko’odinetan hukumar NEMA a shiyyar Kudu-maso-Yamma, Ibrahim Farinloye, a safiyar Lahadi, ya ce an ceto jimillar mutane 20 da ginin ya rufta musu.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), wacce da farko ta bayar da rahoton mutuwar mutum guda yayin aikin ceton a ranar Asabar amma a yau Lahadi, ta ce, adadin yanzu ya kai Biyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp