Rukunin farko na ‘yan Nijeriya da aka kwaso daga kasar Sudan sakamakon yakin da kasar ke ciki sun iso Nijeriya inda suka hadu da ‘yan uwansu da jami’an Gwamnati cikin farin ciki da annashuwa.
Daliban da aka kwaso ta hanyar amfani da filin Jirgin kasar Egypt, sun sauka a Abuja ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Laraba kamar yadda ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ta sanar.
‘Yan Nijeriyan wadanda suka sauka a filin Jirgin kasa da kasa ta Nnamdi Azikiwe a cikin jirgi mallakin sojojin saman Nijeriya da na Air Peace.
A lokacin da take karbar mutanen a filin jirgin, Darakta sashin kula da ‘yan gudun hijira ta hukumar kula da da ‘yan gudun hijira da kaura kasa, Misis Catherine Udida, ta ce jirgin Airforce C130 ne ya kwashe mutane 94, yayin da Air Peace ya kwashe mutane 282
Shugaban ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje, (NiDCOM), Mrs. Abike Dabiri-Erewa, ta ce, an samu gagarumar tarba cikin murna ga ‘yan kasan lura da halin da suka samu kansu da yadda aka yi ta jin labarin suke ciki a can kasar ta Sudan.
Ministar Jin Kai, Hajiya Sadiya Umar Farouq, babban Sakataren ma’aikatar, Dr Nasir Sani-Gwarzo, darakta Janar na hukumar NEMA, Mustapha Habib, da jami’an tsaro hadi da wasu daga cikin iyalan dalbannne suka tarbesu a filin Jirgin.
Majiyoyi sun shaida cewar ‘yan Nijeriyan da suka dawo sun Yi murna matuka tare da iyalansu bisa yadda suka tsinci kansu a cikin kasar Sudan na mawuyacin hali da wahalar da suka sha wajen fitowa daga Sudan zuwa iyakar kasar.
Rikicin kasar Sudan dai zuwa yanzu ya lakume kusan rayuka 600 da tilasta wa dubbai kaura daga muhallansu sannan kasashen da dama suna ta kwashe ‘yan kasuwarsu da ke rayuwa a can.