Rukuni na 5 na wasu na’urorin da aka kafa a tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa da ake kira “Lower Kefu Gorge”, wadanda kamfanin kasar Sin ya gudanar da aikin su a kasar Zambiya, sun fara aiki a jiya Jumma’a 24 ga wata, inda shugaban kasar, Hakainde Hichilema ya halarci bikin kaddamar da aikin.
Cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin, shugaba Hichilema ya ce ginawa, gami da fara amfani da tashar, zai taimaka gaya ga samar da ci gaban tattalin arzikin kasar.
Tashar Lower Kefu Gorge tana kan kogin Kafue, mai tazarar kilomita 90 daga kudancin Lusaka fadar mulkin kasar Zambiya. Ya zuwa yanzu, daukacin rukunonin na’urorin biyar, sun riga sun fara aikin samar da wutar lantarki, al’amarin da zai iya kara samar da kashi 38 bisa dari na makamashin wutar lantarki ga kasar.
A matsayin aiki na abun koyi ga gine-ginen shawarar “ziri daya da hanya daya”, tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta “Lower Kefu Gorge” na taimakawa matuka wajen daidaita matsalar karancin wutar lantarki a Zambiya, da samar da isasshiyar wutar lantarki ga Zambiya, har ma ga sauran kasashen kudancin nahiyar Afirka, tare kuma da samar da ci gaba ga tattalin arziki, da zaman rayuwar al’ummun kasar. (Murtala Zhang)