Kakakin rundunar sojojin ‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar, babban kanar Shi Yi, ya ce a Larabar nan rundunar ta kaddamar da wani atisayen soji mai taken “Strait Thunder-2025A”, a yankunan tsakiya da kudancin zirin Taiwan. Tun a jiya Talata ne rundunar ta PLA ta fara gudanar da atisayen soji a sassan zirin na Taiwan.
Da yake karin haske game da batun, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce atisayen wani gargadi ne mai karfi ga sassan dake rajin neman “‘yancin kan Taiwan”, kana mataki ne halastacce da ya wajaba a aiwatar domin kare ikon mulkin kai da dinke sassan kasar Sin.
- Kasar Sin Za Ta Yi Ramuwar Gayya Kan Takunkumin Biza Da Amurka Ta Kakaba Wa Jami’anta
- Trump Na Son Yin Wa’adi Na Uku Na Shugabancin Amurka
Guo ya kara da cewa yankin Taiwan bangare ne na kasar Sin da ba za a iya balle shi ba, kuma batun yankin harka ce ta cikin gidan kasar Sin da ba ta bukatar tsoma bakin wani bangare na waje.
Ya ce gwamnatin jam’iyyar DPP a Taiwan ta dage kan batun neman “‘yancin kan Taiwan”, tana ta yunkurin neman goyon bayan sassan ketare don cimma nasarar ajandarta da fatan raba kasa. To amma wannan yunkuri ne da ba zai yi nasara ba. Kazalika, ba wanda zai iya dakatar da aniyar kasar Sin ta dinke dukkanin sassanta waje guda. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp