Rundunar sojin ’yantar da al’ummar kasar Sin(PLA) ta yankin gabashi, ta yi nasarar kammala dukkan ayyukan da aka tsara na atisayen hadin gwiwa da aka gudanar a ranakun Talata da Laraba, kamar yadda mai magana da yawun rundunar da ta yi atisayen, babban kanar Shi Yi ya bayyana.
Shi Yi ya ce, dakarun rundunar atisayen na ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana, kuma za su ci gaba da karfafa shirye-shiryen yaki tare da samun kwakkwaran horon soji don dakile duk wani yunkurin ballewa na neman ’yancin kai na Taiwan.
- ‘Yansanda Sun Gayyaci Shamakin Kano Kan Zargin Karya Dokar Haramta Hawan Sallah
- Janar Tsiga Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Bayan Shafe Kwanaki 56 A Hannun ‘Yan Bindiga
An kuma bayar da rahoton cewa, Amurka, da Tarayyar Turai, da Japan da sauransu sun yi tsokaci kan atisayen na hadin gwiwa da sojojin ’yantar da al’ummar kasar Sin suka gudanar a kusa da tsibirin Taiwan a ranar 1 ga watan Afrilu, inda suka zargi kasar Sin da yin barazanar da ba ta dace ba, da karin matsin lambar matakin soji a tsibirin Taiwan ba tare da wasu kwararan dalilai ba.
Dangane da haka, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a taron manema labarun da aka saba yi a-kai-a-kai, da ya gudana yau 2 ga watan Afrilu cewa, batun Taiwan tsantsar lamari ne na cikin gidan kasar Sin kurum, kuma ba a yarda da tsoma bakin ’yan-ba-ni-na-iya daga waje ba.
Kana ya ce, abun da ke kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan shi ne hadin baki da goyon bayan ayyukan masu fafutikar ballewar Taiwan daga wasu rundunoni na waje. Kuma idan har da gaske ne kasashe da kungiyoyin da abun ya shafa suna fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan, kamata ya yi su bi tsarin kasa da kasa da aka aminta da shi wajen kiyaye ka’idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kiyaye alkawuran siyasa da aka yi wa kasar Sin, da mutunta ikon mallakar kasa da ’yancin kan Sin da yankunanta, da kuma nuna adawa da duk wani nau’i na “’yancin kan Taiwan.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp