Rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Daji ta kai wasu hare-haren bama-bamai ta sama inda ta yi nasarar lalata maboyar ‘yan ta’addan tare da kashe wasu da dama a jihohin Katsina da Zamfara.
Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, AVM Edward Gabkwet wanda ya bayyana hakan, ya ce, rundunar ta kai hare-haren ne a ranar 5 ga watan Maris, 2024 a maboyar fitaccen shugaban ‘yan ta’addan – Maudi-maudi da ke kudu da Tsaskiya a cikin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 88 Kan Aikata Laifuka A Katsina
- Kishi: ‘Yansanda Sun Cafke Ma’aikacin Lafiya Da Yunkurin Hallaka Ma’aurata A Bauchi
AVM Gabkwet ya ce, hare-haren an samu nasarar kai su ne ta hanyar amfani da bayanan sirri da aka samu a yankin da ke tsakiyar duwatsu.
“Ko da cewa, an kashe ‘yan ta’addan da dama, amma har yanzu ba mu da tabbacin mutuwar Maudi-maudi sakamakon harin” in ji AVM Gabkwet.
Ya c, an kuma gudanar da irin wannan hare-haren a ranar 6 ga watan Maris, 2024 a sansanin wani fitaccen sarkin ‘yan ta’adda, Alhaji Na-Shama, da ke gabashin kauyen Ussu a cikin gundumar Nasarawar Mailayi a karamar hukumar Birnin Magaji ta Jihar Zamfara.