A ranar 11 ga watan Nuwambar nan ne Rundunar Sojojin Sama ta ’Yantar da Al’ummar Kasar Sin (PLA) ta cika shekaru 75 da kafuwa.
Da yake karin haske a kai, babban jami’in yada labarai na Rundunar Sojin Saman ta PLA, Babban Kanar Xie Peng, ya yi bayanin cewa, domin murnar wannan rana, rundunar ta shirya bukukuwa daban-daban ciki har da Bikin Shawagin Sararin Sama na Kasar Sin karo na 15 domin nuna bajintar tuka jiragen sama, da nuna kafaffun manyan makaman soji da kuma kade-kade da wake-waken sojoji da sauransu.
Rundunar sojin za ta aike da kayan aiki daban-daban guda 36 zuwa bikin shawagin sararin saman da kuma kafaffun makaman da za a nuna. Daga cikin wadanda za su gwangwaje bajintarsu a bikin, akwai tawagar masu nuna fasahar tuka jiragen sama ta Bayi da ta Red Eagle, da kuma jirage 26 masu samfura daban-daban guda 7, ciki har da jiragen yaki masu samfurin J-20, da J-16 da kuma na YY-20A. (Abdulrazaq Yahuza Jere)