Bisa labarin da ma’aikatar harkokin albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, ana sa ran cewa, fadin sabbin gonakin da za a shawo kan matsalar zaizayewar kasa a Sin a karshen shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 ya kai muraba’in kilomita dubu 340, fadin gonakin da aka tabbatar da yanayin ruwa da kasar da ke cikinsu ya kai kashi 73 cikin dari.
Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, a yayin gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, an kiyaye kyautata yanayin zaizayewar kasa a kasar Sin, kuma an cimma burin rage fadin gonakin da suka gamu da matsalar, da kuma rage illar da ruwa da iska suka haddasa wa gonaki.
Alal misali, a yankin Loess Plateau na kasar Sin, hukumomin kula da harkokin albarkatun ruwa sun maida hankali ga tabbatar da yanayin duwatsu da ruwa da bishiyoyi da tabki da ciyayi da rairayi, kuma an kafa tsarin kiyaye yanayin ruwa da kasa, da tsara yankuna mafi maida hankali ga kiyaye yanayin ruwa da kasa bisa doka, da kuma daukar matakan daidaita da magance matsalar zaizayewar kasa.
Hakazalika, hukumomin albarkatun ruwa sun yi hadin gwiwa tare da hukumomin da abin ya shafa a kan gabatar da jerin manufofi kamar su neman cimma adadin samar da kayayyaki daga halittun muhalli da kiyaye yanayin ruwa da kasa, da sa kaimi ga zuba jari ga aikin daidaita matsalar zaizayewar kasa da sauransu, don fadada hanyoyin samun wadata ta hanyar kiyaye muhallin halittu. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp