Mahukuntan birnin Addis Ababa a fadar mulkin kasar Habasha, sun samar da motoci kirar Bas masu aiki da lantarki guda 100, domin sufurin fasinjoji a sassan birnin, a wani mataki na bunkasa amfani da ababen hawa masu aiki da lantarki a kasar dake gabashin Afirka.
Kafar watsa labarai ta kasar ta ce kamfanin cikin gida mai suna Belayneh Kindie Metal Engineering Complex ne ya kera motocin da sassan da aka shigo da su daga kasar Sin, kuma motocin na dauke da na’urorin zamani masu taimakawa wajen gudanar da aikin sufuri na zamani, da fasahar biyan kudaden sufuri cikin sauki.
- Tinubu Ya Kori Mele Kyari, Ya Naɗa Ojulari A Matsayin Shugaban NNPC
- Trump Na Son Yin Wa’adi Na Uku Na Shugabancin Amurka
Tuni dai motocin suka fara bin tashoshin musamman na zirga-zirgar fasinjoji masu inganci da aka tanada a sassan birnin Addis Ababa.
Da yake tsokaci kan haka, ministan sufuri da aikewa da sakwanni na kasar ya ce a halin yanzu, motoci masu aiki da lantarki sama da 100,000 ne ke zirga-zirga a titunan kasar, kuma gwamnati na da burin kara yawansu zuwa 500,000 cikin shakaru 10 masu zuwa, inda ake fatan maye gurbin kaso 95 bisa dari na ababen hawa masu aiki da mai a kasar.
Domin hanzarta cimma wannan buri, tun a farkon shekarar bara, gwamnatin Habasha ta sanya takunkumin hana shigar da ababen hawa masu amfani da man fetur da man dizal cikin kasar, a gabar da farashin man ya fara hauhawa a kasuwannin duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp