An rufe taron Davos na lokacin zafi karo na 14 a birnin Tianjin na kasar Sin a jiya Alhamis, inda Sin din ta ce za ta samar da sabbin damarmaki ga duniya ta hanyar sabbin nasarorin da za ta samu a tafarkin da ta dauka na zamanantar da kanta.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ce ta bayyana haka, inda ta ce, tun daga farkon bana, tattalin arzikin Sin ke samun tagomashi kuma ana sa ran ya bunkasa da kaso 5 bisa dari a baki dayan bana. Kana a cikin watanni 5 na farkon bana, sabbin kamfanonin jarin waje da aka kafa a fadin kasar Sin sun kai 18532, adadin da ya karu da kaso 38.3.
Mao Ning ta kuma bayyana cewa, mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, zai halarci bikin bude taron duniya kan zaman lafiya karo na 11 da za a yi a ranar 2 ga watan Yuli, tare da gabatar da jawabi. Taron mai taken “Neman cimma matsaya, inganta hadin gwiwa da tabbatar da oda da kare zaman lafiya”, zai gudana ne a jami’ar Tsinghua dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)