Rasuwar Malam Sabo Ahmad Kafinmaiyaki gibi ne mai wuyar cikewa a cikin al’umma. A iya zaman da na yi shi na karu da abubuwa da dama musamman a fannin aikin jarida.
A lokacin da yana Editan LEADERSHIP A Yau Lahadi, Malam ya kan zaunar da ni kamar abokinsa mu tattauna akan abin da ya shafi aiki da zamantakewa, a irin wannan zama da mu kan yi da shi yake bani labarin dangantarsa da Jihar Kano, inda ya ce ai shi dan asalin Jihar Kano ne, a unguwar Yakasai dake yankin Karamara Hukumar Birnin da kewaye wato Kano Municipal, har ma yake ce min iyayensu su ne asalin masu unguwar Yakasai, kuma har yanzu idan ya je Kano ba ya fara zuwa ko ina sai Yakasai ya sadar da zumunci koda kuwa bai wani abin ne ya kai shi daban.
- Cire Tallafin Mai Ya Dace, Amma A Gaggauta Saukaka Wa Al’umma
- Hukumar GEIDCO Ta Zayyana Ayyuka Da Za A Samar A Afirka
Kafin ya zama Editan Jaridar LEADERSHIP a sashen Hausa, Malam Sabo ya kafa jarida tasa ta kansa mai suna Aljazira, wacce shi kadai ne yake gudanar da ita da aljihunsa da tunaninsa da kuma sauran wadanda suke taimaka masa. Ganin wannan hazaka tasa ta sa aka neme shi domin ya ba da gudunmawa a LEADERSHIP, a lokacin da kamfanin ya bude sashen Hausa da za ta rika fita a kullum wato LEADERSHIP A Yau, karkashin jagorancin marigayi Sam Nda Isiah, wanda kuma shi ya kafa kamfanin, wanda Editocin jaridar suka hada da Sulaiman Bala Idris a matsayin Editan jaridar da za ta rika fita kullum, wanda daga karshe ya samu ci gaba izuwa daraktan sashen Hausa, wanda a yanzu shi ne Sakataren Yada Labarai na zababben Gwamnan Zamfara.
Sai kuma Malam Abdurrazak Yahuza Jere, a matsayin Editan ranar Juma’a, Mubarak Umar Abubakar, shi ne Editan ranar Asabar, wanda shima daga baya ya samu karin girma zuwan Draktan sashen Hausa na jaridar, kafin daga bisani Sulaiman Bala Idris ya zama daraktan sashen.
A bayan da Mubarak ya samu ci gaba ne sai aka nemo Malam Sabo domin ya maye gurbinsa a matsayin Editan jaridar ta ranar Asabar.
Daga baya kuma kamfanin ya sauya tunaninsa bayan rasuwar marigayi Sam inda aka sake dawo da jaridar asalin matsayinta na da wato LEADERSHIP Hausa.
Wannan canji da aka yi, ya sanya a rushe dukkanin Editocin guda uku, bayan da maidakin marigayi Sam wato Mis Zainab Nda Isiah ta karbi jan ragamar kamfanin, wanda a halin yanzu Malam Abdurrazak Yahura Jere shi ne Babban Edita a sashen LEDAERSHIP Hausa.
Abin da ya sa na kawo wannan dan gajeren tarihin domin mu dubi irin hakuri na Malam Sabo, wanda yana matsayin Edita aka dawo da shi matsayin shugaban sashen fassara da bin diddigi, amma hakan bai sa ya ki karbar matsayin ba duk yana kasan wancan matsayi nasa na farko, da hakan ya ci gaba da biyayya gami da karbar umarni daga babban Edita Abdurrarak Yahuza Jere, haziki kuma jajirtacce.
Zan iya cewa Malam Sabo yana daga cikin mutanen da na tabbatar irinsu a cikin al’umma daban ne. Sannan shi mutum ne mai amana da gaskiya, ga kawaici, in dai ana zaune a wurin aiki duk irin hirar da ake yi idan har ba ta shafe shi ba, zai yi wuya ka ji ya tsoma baki.
A duk lokacin da zai tafi sayo abinncin dare ko rana ko na safiya sai ya tambayi kowa shin akwai mai sako? Idan akwai mai sako haka za a tara masa kudin abincin mafi aksarinmu duk ya grime mu amma haka zai karbi kudinmu ya tafi ya sayo, ka ganshi da abinci da yawa a hannunsa. Muma mu kan je mu sayo, amma dai abin dubawa shi ne yadda yara irinmu da ya sa ya grime mu amma ba ya kyashin ya karbi sakonmu ya amso mana wani abin aike, a nan kuma rashin girman kai yake nunawa.
To a irin wannan sayo abincin ne ya tafi Utako ya sayo wa abokan aiki abin muda baki, ya yanke jiki ya fadi, wanda tun da ya yi wannan faduwa Allah bai kaddara masa tashi ba.
Kusan in ce wannan shi ne kadan daga abin da zan iya tunawa a halayyarsa a zaman da na yi da shi, amma idan masu karatun na bibiyar shafin bayan jaridar nan za su ga sauran abokan aiki na ci gaba da fadar halayensa.
Malam Sabo ya yi aiki a tsakanin zakakuran Editoci matasa.
Muna addu’ar Allah ya ji kansa da rahma ya kyautata makwancinsa ya saka masa da mafificin alheri, ya shiryi bayansa, ya ba wa iyaye iyalai, ‘yan uwa da abokan arzikinsa da mu abokan aikinsa hakurin juriyar wannan babban rashi.
Allah ya jikan dukkanin al’ummar Musulmi da suka riga mu gidan gaskiya ya bamu sa’ar tad da su ya sa mu yi kyakkyawan karshe.
Idris Aliyu Daudawa: Allahu akbar, Allahu akbar, Kullu nafsin za’ikatul maut,
Wannan al’amarin haka yake daukacin duk mai rai wata rana shi ma zai koma ga mahaliccinsa da zarar lokacin komawarsa ya yi, haka abin zai kasance babu karin wani lokaci ko da kuwa dakika daya ce.
Al’amarin rayuwa ke da haka sai dai babbar fatan da kowa yake kullum shi ne ya cika da imani wato kalmar shahada wacce ba karamar nasara bace mutum ya cika da ita.
Wannan rubutu mun yi shi ne saboda rashin abokin aikinmu Sabo Ahmed Kafin Maiyaki, da Allah ya yi ma sa rasuwa yau kwana 22 da suka gabata ke nan, bayan ya yi fama da rashin lafiya a inda aka kwantar da shi a Asibitin Sabana dake Zariya.
Ya rage saura kwana biyu a yi karamar Sallah wato ranar Laraba kenan bayan da aka kammala bin diddigi na dukkan shafukan Jaridar LEADERSHIP Hausa kafin a kai ga wallafa ta, lamarin ya faru a cikin watan azumin Ramadan, kamar yadda muka saba yi mu kan je sayo sayen abincin buda baki tare da shi muka tafi muna tafiya muna ta hira ganin ga karamar Sallah ta matso domin a lokacin sauran kwana biyu, saboda an yi ta ranar Juma’a ne, a nan wurin sayen abincin ne muna tsaye ya yanke jiki ya fadi.
Ganin haka ta faru tun da lokacin hankalina ya tashi, nan da nan sai na kira Malam Bello Hamza da Rabi’u Ali Indabawa suka zo daga ofis inda muka dauke shi tare da wani yaro Zarahaddini zuwa wani asibiti domin bashi agajin gaggawa, inda ya kwana a wannan asibiti.
Washegari ranar Alhamis Malam Bello ya sanya shi a mota aka tafi da shi Zariya inda ba a zame ko ina ba sai asibiti.
A tsawon shekara shida da muka kasance da marigayi Malam Sabo, na sani mutum ne wanda yake da matukar hakuri da kawaici kunya da yakana domin kuwa zai yi matukar wuya ya ka ga abin da zai bata masa rai, a ko da yaushe ya kan so ya rika ba wa mutum shawara, shawararsa ba ta wuce mutum ya rika yin hakuri da al’amuran duniya saboda wata rana ai sai labari.
Mutum ne da ba shi da girman kai saboda duk yadda kake zai saurare ka koda wata shawara ce daga wurinsa zai baka wadda idan ka yi amfani da ita ba za ka yi nadama ba.
Akwai shi da kokarin karfafa sada zumunci
Lokaci zuwa lokaci yana tafiya kafin Maiyaki wajen ‘yan uwansa ko kuma taron kungiyarsu ta tsofaffin dalibai na makarantar Sakandare ta Kafin Maiyaki. Ya kan je ne karshen wata ko bayan ‘yan makonni.
Ta bangaren aiki ana iya cewa hazikin ne saboda ilmin da yake da shi a fannin Turanci da Hausa wadda ko ta wanne fanni in ka nemi shawara shi zai baka musamman ma idan yana magana kana sauraren sa kamar yadda ya dace, gaskiya ba karamin rashi aka yi ba, daga iyalansa da kuma sauran ‘yan’uwansa da abokan huldarsa.
Fatan kowa shi ne Allah ya yafe masa kura- kurensa da ya aikata, mu kuma idan tamu ta zo mu cika da imani. Ba ni kadai ba daukacin sauran ‘yan’uwa ma’aikatan bangaren LEADERSHIP Hausa sun karu matuka da basirarsa ta bangaren Hausa da aikin Jaridar.