Zababen Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare a ganawarsa ta farko da manema labarai jim kadan bayan tabbatar da shi a matsayin zababen Gwamnan Jihar Zamfara, ya yi alkawarin magance matsalolin da suka addabi al’ummar Jihar.
Ya kara da cewa, al’ummar Jihar Zamfara sun nemi canji kuma cikin kudirar Allah ya amsa addu’arsu sakamakon jajircewarsu da suka yi.
- Magoya Bayan Peter Obi Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Abuja Kan Zaben 2023
- 2023: Jihohin Da INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnoni
“Dauda ya kuma tabbatar da cewa, gwamantisa za ta yi iya kokari wajen magance tsaro da bunkasa Nlnoma da kasuwanci da ilimi da sauransu.
Zababen gwamnan ya ja kunnen matasa da subi doka da oda, wajen taya shi murnar samun nasara.
A karshe zababen gwamnan ya mika godiyarsa ga al’ummar Jihar Zamfara da suka jajirce wajen kawo canjin gwamnati.