Shugaban Kasar Rasha Bladimir Putin ya karbi wasikar jakadanci ta sabon jakadan Nijar a kasar Rasha a fadar Kremlin dake Birnin Moscou.
Gwamnatin Nijar, a yayin wani zaman taron ministoci na ranar 15 ga watan Mayun shekarar 2024, ta amince da nada Janar Abdou Sidikou Issa a wannan muhimmin matsayi, wanda kuma hakan ya nuna cewa, tsohon shugaban rundunar sojojin Nijar, Janar Abdou Sidikou Issa zai wakilci bangaren diplomasiyyar Nijar a kasar Rasha.
- EFCC Ta Gurfanar Da Tsofaffin Gwamnoni Da Tsofaffin Ministoci, Bayan Kwato Kadarorin Biliyoyin Naira A Kasashen Waje
- Ainihin Nufin Philippines Na Kafa Abin Da Take Kira Dokar Yankunan TekuÂ
Inda ya mika takardar jakadancinsa ga shugaban Kasar Rasha Bladimir Putin a Nuwamban shekarar 2024.
Shi dai tsohon manjo-janar din sojojin Nijar, Abdou Sidikou Issa, sananne ne a fagen siyasar Nijar, kuma mutum ne mai son aiki, da ya taka muhimmiyar rawa a lokacin juyin mulkin ranar 23 ga watan Yulin shekarar 2023.
Kazalika a 2024, ministan sadarwa Sidi Mohamed Raliou ya gana da dukkan wakilan gidajen rediyo, talabijin da jaridu na kasashen waje dake aiki a Nijar, ganawar da ta gudana a ofishin ma’aikatar sadarwa dake Birnin Yamai.
Wannan ganawa irin ta ta farko, ta kasance wani tsarin tattaunawa, da yin musaya kan batutuwa da dama da suka shafi tsinkayen shugaban kwamitin ceton kasa da kuma daidaita matsayin wakilai da aikinsu a Nijar.
Ministan sadarwa ya bukaci ganin goyon bayan wakilan kafofin watsa labarai na kasashen waje dake Nijar game da hangen shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP Abdourahamane Tiani da ya rataya kan zaman jituwa tsakanin al’ummar kasa, tsaro da kuma mulki na-gari.
Haka zalika, minista Sidi Mohamed Raliou ya ja hankalin wadannan ‘yan Nijar dake ma kafafen sadarwa na kasashen waje aiki a Nijar, da su kasance masu kishin kasa, da su sanya moriyar kasarsu a gaba, da kuma fifita ci gaban kasarsu.
A nasu bangare, mahalarta wannan ganawa sun nuna jin dadi da gamsuwarsu game da wannan tunani na ma’aikatar sadarwa bisa ga shirya wannan haduwa.
Haka kuma, sun yi amfani da wannan dama, domin bayyanawa minista Sidi Mohamed Raliou, matsalolin da suke fuskanta game da neman labarai daga wajen hukumomi, da kuma fatan ganin an daidaita wadannan matsaloli.
Daga karshe, minista Sidi Mohamed Raliou, ya tabbatarwa wadannan ‘yan jarida niyyarsa na rakiyarsu da kuma kasancewa mai saurarensu a kowane lokaci, tare da yin musanya kan batutuwan da za su taimaka musu tafiyar da aikinsu cikin sauki kuma cikin girmama ka’idodin aikin jarida.