Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce bisa gayyatar da aka yi masa, ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, zai ziyarci kasashen Habasha, da Gabon, da Angola, da Benin, da Masar, da kuma helkwatar kungiyar tarayyar Afirka AU, da helkwatar kungiyar kasashen Larabawa tsakanin ranaikun 9 zuwa 16 ga watan nan.
Wang Wenbin ya ce wannan ziyara ce ta farko da Qin Gang zai kai kasashen ketare, tun bayan kama aikin sa a matsayin ministan wajen kasar ta Sin. Kaza lika bana ce shekara ta 33 a jere, da ministan wajen Sin ke kai ziyarar aiki ta farko a duk shekara kasashen Afirka.
Yayin ziyarar ta wannan karo, Qin Gang zai gudanar da taruka da shugabanni, da ministocin wajen kasashe 5 da zai ziyarta, da shugaban hukumar zartaswar AU, inda zai yi musayar ra’ayi da su game da alakar Sin da sassan, da sauran batutuwan dake jan hankulan su a matakin kasa da kasa da na shiyyoyi.
Har ila yau, bisa tsarin ziyarar ta sa, a kasar Masar Qin Gang, zai gana da babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp